N’KONNI, NIGER - Sai dai, kungiyoyin malaman makarantun bokon kasar sun ce suna da shakku game da wannan alkawarin da aka dade ana yin irin sa ba cikawa.
Ministan ilmi na Jamhuriyar Nijar ya ce, gwamatin kasar ta saka kudade a kasasfin bana da na shekara mai zuwa da ya kai billiyan 96 na Sefa domin gina makarantu na dindindin, ta la'akari da yawan gobara da aka fuskanta a ‘yan shekarun baya-baya a cikin ajujuwan zamaki da suka kai ga asarar rayukan dalibai da ma jikkata da dama a babban birnin Yamai da wadansu jihohin kasar.
Ministan ilmi Ibrahim Na Tatu, ya yi wannan sanarwar ne, a lokacin komawa ajujuwan karatu na boko na wannan shekara.
Gina ajujuwa na dindindin na karatun boko, za a yi sa gadan-gadan a shekara ta 2022 da shekara ta 2023, shi ya sa ma, aka sassauta ayyukan ‘yan kwangila kan wannan aikin.
Ministan, ya ci gaba da cewa, a cikin kasasfi na kudi na 2022, gwamnati ta ware sefa biliyan 18, yayin da ta ware biliyan 78 a cikin kasasfin kudin shekara ta 2023 domin gina ajujuwa na dindindin, kuma dadin dadawa in ji minista Na Tatu, masu hannu da shuni su ma za su gina wadansu ajujuwan domin tallafawa gwamnati.
Sai dai, a cewar kungiyoyin malaman makarantun boko na kasar, kamar SNEN, magatakardan ta a gundumar birnin N'Konni Habibu Mumuni, ba fada ba, cikawa.
Saurari cikakken rahoto daga Haruna Mamane Bako: