Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Iyakar Najeriya Da Nijar


Yan Bindiga
Yan Bindiga

Yayin da a ke kara matsawa zuwa lokutan fara zabubukan gama gari a tarrayar Najeriya, maganar tsaro na ci gaba da daukar hankullan al'ummar, musamman a Arewacin kasar.

BIRNIN N’KONNI, NIGER - A sanyin saiyar ranar Laraba, an tashi a kan iyakar Nijar da Najeriya da kararar bindigogi m a garin Jema dake cikin karamar hukumar mulkin Illela ta Jihar Sakkwato. Garin Jema na Najeriya dai kunyar noma ce ta raba shi da Jema na Jamhuriyar Nijar.

Yan Bindiga
Yan Bindiga

Bayan mutanen garin sun fatattaki ‘yan bindigar da suka jiwa mutan biyu rauni dake kan hanyar zuwa kasuwar Illela, sun bar su a cikin halin rai ko mutuwa, bayan haka ne mazamna garin na Jema suka fatatttaki ‘yan bindigan inda suka kashe mutane hutu, kamar yanda wani mutumen Kalmalao ya bayyanawa sashen Hausa.

A lokacin da aka tuntubi daya daga cikin rundunonin tsaron wannan yankin, sun tabbatar da aukuwar lamarin, amma suka ce basu da hurumin yin magana halin yanzu, har sai sun kamalla bincike da ma neman wadanda suka aikata wannan danyen aikin.

Yan bindiga a jihar Sokoto
Yan bindiga a jihar Sokoto

Shin a cikin wannan halin yaya za'a gudanar da zabuka a wadanan yankunan, ita ce tambayar mu ga mutumen Kalmalao.

A wata hira ta wadansu ma'aikatan INEC da aka baiwa horo a wannan iyakar, sun tabbatar da cewa idan har a ka aika su yankuna masu matsalar tsaro ba za su je ba.

A yayin da mutan biyu da suka ji rauni, an tura su zuwa assibitin kasa da kasa na Galmi a cikin gundumar Malbaza a Jamhuriyar Nijar, yayin da a ke can ana jana'izar mutane hudu da ‘yan bindiga suka hallaka a lokacin hada wannan rahoton.

Saurari cikakken rahoto daga Harouna Mamman Bako:

Ana Gab Da Babban Zaben Najeriya, ‘Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Kan Iyakarta Da Nijar.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:08 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG