Biyo bayan kalaman da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi jim kadan bayan rantsuwar kama aiki na mayar da birnin kan taswirarta na asali, wasu masu kananan sana’o’i na neman a yi nazari kar a jefa su cikin matsin rayuwa.
‘Yan Najeriya da dama dai sun fara dasa alamar tambaya a kan ko Shugaba Tinubu zai rika martaba tsarin mulkin dimokradiyya.
A daidai lokacin da wani sauti ke yawo a kafafen sada zumunta kan wani shirin gwamnatin Najeriya na raba tallafi ga 'yan kasa ta hanyar asusun E-Naira na babban bankin Najeriya, bankin CBN ya karyata labarin.
Ana sa ran wannan aiki zai samar da Megawatt 350 cikin 1, 350, wanda ya kasance kashi na farko na baki dayan aikin.
Duk da cewa wasu dattawa karkashin kungiyar hadin kan Arewa, Northern Alliance Committee sun nuna goyon baya ga tsare-tsaren gwamnatin Bola Tinubu, dattawan sun mika bukata cewa ya mayar da hankali wajen fitar da shirin rage radadin cire tallafin man fetur.
Babban bankin Najeriya wato CBN ya kara kudin ruwa da maki 25 na kaso 1 bisa 100 wanda ke nufin an yi karin daga kaso 18 da digo 5 zuwa kaso 18 da digo 75 cikin 100.
Masanan sun yi nuni da bukatar ganin an tuhume shi da sauran laifukan da ake zargin ya aikata baya ga na mallakar makamai.
'Yan Najeriya n ci gaba da kokawa a kan karin farashin litar mai da aka yi, baya ga shirin yin gagarumin kari a kudin wutan lantarki, da kuma sanarwar da gwamnati ta fitar na yin kari a kan kudin makarantar kwalejojin sakandare na gwamnatin tarayya.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya tare da hadin gwiwar ma’akatar kudi da tsare-tsare suka kira taron gaggawa a kan yanayin da ake ciki, inda aka cimma matsayar hadin gwiwa da dukan masu ruwa da tsaki a kasar don samo mafita mai dorewa kan matsalar karancin abinci.
A yau talata ne al’ummar Najeriya musamman a manyan birane ciki har da Abuja, Legas, Kano, Kaduna da dai sauransu, suka wayi gari da tashin farashin man fetur daga naira 537 zuwa naira 617 ko wace lita.
Hukumar kwastam ta bayyana hakan ne a wani taron karawa juna sani na yini biyu da ta shirya a birnin tarayya Abuja.
Wata babbar kotu dake da zamanta a birnin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin mai shari’a James Omotosho ta amince da bukatar bada belin dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, wato DCP Abba Kyari.
A daidai lokacin da ake dakon jerin sunayen wadanda shugaban Najeriya Bola Tinubu zai mika ga majalisun tarayyar kasar don tantancewa da amince da su a matsayın ministocinsa, ‘yan asalin birnin Abuja sun mika koke ga shugaban da ya waiwaye su ya nada dan asalin garin a matsayin ministan Abuja.
Domin Kari