Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Bin Umurnin Kotu Da Gwamnati Ke Yi Na Zub Da Darajar Najeriya Ne A Idon Duniya - Masana


‘Yan Najeriya da dama dai sun fara dasa alamar tambaya a kan ko Shugaba Tinubu zai rika martaba tsarin mulkin dimokradiyya.

Sama da watannin biyu da tsare dakataccen shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa ba tare da tuhuma ba da kuma ci gaba da kin mutunta umurnin kotu na a saki Godwin Emefiele, masana shari’a sun bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa yancin shari’a ya zama sahihi kar a koma gidan jiya na tsare mutane da ake zargi da aikata laifi ba bisa ka’ida ba don kawo sauyi da ake bukata na yin garambawul a yanayin gudanar da shari’a a kasar.

Dakataccen Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa - a dama (Instagram/EFCC)
Dakataccen Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa - a dama (Instagram/EFCC)

Batun tsare wadanda ake zargi da aikata laifi ba bisa ka’ida ba a Najeriya dai ya kara kamari ne a shekarun baya-bayan nan musamman a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari duk da cewa jim kadan bayan karbar mulkinsa a shekarar 2015 ya jaddada aniyarsa ta tabbatar da cewa dukkanin hukumomin gwamnatin da ke karkashin gwamnatinsa suna bin doka da oda.

Saidai duk da kalaman shugaba Buhari da mataimakinsa a waccan lokacin, gwamnatinsa ta bijire wa umurnin kotu a lokuta da dama na a saki tsohon mai bai wa Goodluck Jonathan shawara a kan harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki, wanda aka yi wa zargin karkatar da dala biliyan 2.1 da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Sambo Dasuki
Sambo Dasuki

Ko da yake an bayar da belin Kanar Dasuki a akalla sau shida daga kotuna daban-daban, gwamnatin Najeriya ta ki bin umurnin kotun a lokacin, sai kuma tsare mutane kamar shugaban kungiyar ‘yan shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaki, tsohon alkalin Alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, tsohon sakataren yada labaran jam’iyyar PDP Olisa Metuh, dan siyasa kuma mai fafutuka, Omoyele Sowore da dai sauransu.

A yanzu dai, rahotanni sun yi nuni da cewa a bisa dukkan alamu shugaba Tinubu na neman dorawa a inda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsaya musamman ganin yadda aka bijire wa umurnin kotun da ta bada belin dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, sai kuma dakataccen shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa Abdulrasheed Bawa, da ake ci gaba da tsarewa ba tare da bayyana laifin da ya aikata karara ba ko kuma gurfanar da shi a gaban kuliya.

Tsohon Shugaban Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele
Tsohon Shugaban Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele

‘Yan Najeriya da dama dai sun fara dasa alamar tambaya a kan ko Shugaba Tinubu zai rika martaba tsarin mulkin dimokradiyyar inda mai Sharhi a kan al’amurran yau da kullum, Mal. Salihu Mahmoud ya ce bijirewa umurnin kotu da gwamnatin nan ta soma yi na da illa ga tsarin mulkin dimokuradiyya sossai.

Jigo a jam’iyyar PDP, sanata Umar Ibrahim Tsauri, ya ce akwai dokoki a Najeriya amma matsalar ita ce rashin aiwatarwa, kuma ba abun mamaki ba ne da aka fara kin mutunta umurnın kotu a gwamnatance saboda shugaba Bola Tinubu ya fayyace cewa zai dora ne a inda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsaya, yana mai cewa rashin mutunta umurnin kotu zai ci gaba da zubar da darajar kasar ne a Idon duniya.

Kazalika wasu ‘yan Najeriya sun fara yada batun cewa akwai alamar gwamnatin da shugaba Tinubu ke jagoranta ta bullo ne da sabon salon kare wadanda ake zargi da yin babakere da kudadden jama’a tare da tozarta masu binciken yaki da matsalar cin hanci da rashawa ganin yadda shugaban ya bai wa tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, goyon baya ya zama shugaban majalisar dattawa a watan Yuni duk da zargin karkatar da kudadden al’umma na Naira biliyan 108 da EFCC ta dade tana yi ma sa, sai kuma nada tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, da takwaran aikinsa na jihar Kebbi duk da ake zarginsu da aikata almundahana.

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle (Facebook/Gwamnatin Zamfara)
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle (Facebook/Gwamnatin Zamfara)

A wani bangare kuwa, wasu masu ruwa da tsaki a kasar na ganin cewa ana siyasantar da batun ci gaba da tsare Abdulrasheed Bawa ne ganin yadda ya far wa wadanda ake zargi da aikata almundahana a kasar kuma a baya shi ma Bawa ya bayyana cewa cin hanci da rashawa da EFCC ke yaki da shi yana mai cewa gyara Najeriya sai da yan kasar.

Shin akwai wani sashen doka da ya amince da batun a tsare wanda ake zargi da aikata wani laifi kamar Godwin Emefiele da gwamnati ta ki ta saka duk da cewa kotu ta bada belinsa da kuma Abdulrasheed Bawa da ake ci gaba da tsarewa sama da sa’o’i 48 ba tare da gurfanar da shi a gaban kotu ba, masanin shari’a, Daniel Bwala, ya ce akwai dokar da jami’an hukumar DSS ke dogara da ita da ta basu damar su tsare mutum na tsawon mako biyu idan suna kan gudanar da bincike.

A nasa bangare, masanin kundin tsarin mulki Barr. Mainasara Kogo, ya bayyana cewa ci gaba da tsare Bawa ba tare da an bayyana laifin da ya yi da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya ba ya yi wa tanade-tanaden sashe na 34 zuwa 37 na dokar kasar karan-tsaye kuma dole sai an yi wa sashe na 230 zuwa na 304 na tsarin mulkin Najeriya garambawul ta yadda za a gyara tsare-tsaren kotunan kasar.

Rahotannin dai sun yi nuni da cewa kama Abdulrasheed Bawa da hukumar DSS ta yi ba ya rasa nasaba da zargin cin hanci da rashawa da kuma taimaka wa Emefiele wajen sake fasalin kudin Naira da ya sanya ‘yan Najeriya cikin matsatsi a watannin farko-farkon shekarar 2023.

Idan Ana iya tunawa dai wannan ba shi ne karon farko da ake dakatar tare da tsare shuwagabannin hukumar EFCC ba inda a baya ma a ranar 6 ga watan Yulin shekarar 2020, an kama tsohon mukaddashin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu da zargin aikata laifin almundahana da almubazzaranci da sunan ofishinsa daga bisani aka kama shi, kuma Magu ya ci gaba da zama a tsare na dan lokaci.

Duk kokarin ji ta bakin hukumar DSS ta wayar Salula da sakon kar-ta-kwana na SMS a yayin hada wannan rahoton dai ya ci tura inda jami’in hulda da jama’arta, Peter Afunnaya, ya bayyana mana cewa yana cikin wani taro don haka a tura masa sako wanda aka yi yadda ya nema amma kuma bai mayar da martani a kai ba.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:55 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG