Kotun ta ba da belin ne bisa dalilai biyu da suka hada da ba'a taba samunsa da aikata wani babban laifi a baya ba, da kuma tsayawa da ya yi a gidan gyara hali na kuje duk da cewa yan ta'adda sun afkawa furson din sun arce.
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi wato NDLEA ce ta gabatar da DCP Abba Kyari a gaban kotu a bisa zargin almundahana da miyagun kwayoyi da aka kama daga hannun wasu baragurbin masu safara.
Idan Ana iya tunawa, a ranar litinin 27 ga watan Maris na shekarar 2022 wanda ya kasance karo na 3 ne babbar kotun tarayya karkashin mai shari'a Emeka Nwite ta yi watsi da bukatar bada belin DCP Abba Kyari, bisa la’akari da hujojjin da NDLEA ta gabatar wanda ya nuna cewa bai dace a bada belinsa ba saboda kwararan bayanai da kuma yanayin shari’ar da ake ma sa musamman ma zargin yiyuwar yin mu'amala da masu aikata laifi idan ya sami beli.
Saurari rahoton cikin sauti: