Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamata Ya Yi Gwamnati Ta Kawo Tsari Da Zai Amfani Kowa - Masana


Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu

'Yan Najeriya n ci gaba da kokawa a kan karin farashin litar mai da aka yi, baya ga shirin yin gagarumin kari a kudin wutan lantarki, da kuma sanarwar da gwamnati ta fitar na yin kari a kan kudin makarantar kwalejojin sakandare na gwamnatin tarayya.

ABUJA, NIGERIA - Masana dai sun ce kamata ya yi gwamnati ta fitar da tsare-tsaren da zasu amfani dukan ‘yan kasan yadda za su sami sauki ba kara kuntata musu ba

Batun yin kira da gwamnatin tarayya da ta sake daura damara ta fitar da sabbin tsare-tsaren da zasu zama mafita ga ‘yan kasar a cikin yanayin matsatsin da suke ciki a yanzu na kara jan hankali ne sakamakon matsaya mai mataki shida na rage radadin cire tallafin man fetur da kwamitin tattalin arzikin tarayyar kasar ya cimma a ranar alhamis data gabata.

Matakan sun hada da tattaunawar yin kari a kan mafi karancin albashi ga ma’aikata; kowace jiha ta yi shirin aiwatar da aikin bada tallafi a bisa tsarin rijistar zamantakewa na jihar, tsarin tallafawa kanana da matsakaitan sana’o’i da dai sauransu lamarin da masana ke ganin kamata ya yi a fara aiwatarwa gadan-gadan don gujewa karin matsaloli a kasar.

Shin ina matsalar take kuma yaya al’umma zasu iya samun sauki a kan wannan al’amari na tsadar man fetur a bisa alkawarin baya, mataimakin shugaban kungiyar dillalan man fetur wato IPMAN, Abubakar Maigandi Dakingari, ya bayyana cewa har yanzu babu wani mamba a kungiyarsu da ya sami lasisin shigowa da mai illa kamfanin NNPCL da kungiyar DAPPMA ke da lasisi.

Ya ce amma kuma da zarar sun sami lasisi za’a ga sauki a harkar farashin kowacce litar mai a kasar, inda suka bukaci ‘yan kasa su kara hakuri, komai zai daidaita nan bada jimawa ba.

Dr. Yakubu Sani Wudil kwararre a fannin makamashi kuma malami a Jami’ar Sarki Fahad dake kasar Saudiyya ya ce kamata ya yi gwamnatin Najeriya ta sake fitar da sabbin tsare-tsaren kawo sauki da zai taba dukkan ‘yan kasar saboda tsarin tallafin ake kokarin aiwatar wa na ‘yan kalılan ma’aikatan gwamnati ne kawai.

Ya kara da cewa kamata ya yi a bada karfi ga gyara matattun man kasar da kuma samar da sabbi.

Shi ma masani a fannin albarkatun man fetur, Muhammad Saleh, ya ce kamata ya yi gwamnatin tarayya ta tuntubi kamfanin NNPCL a kan batun tsarin makamashi na CNG don samun wata hanyar makamashi na daban don a yanke ci gaba da dogaro ga man fetur kawai ba wai bada tallafin dubu takwas-takwas da ba zai kai ko’ina ba.

A yayin da ’yan Najeriya ke neman hanyoyin da za su bi don samun sauki a yanayin da ake ciki da sabon yanayin tattalin arzikin kasar sakamakon cire tallafin man fetur da sabuwar gwamnati ta yi, masana tattalin arziki kamar su Bismack Rewane sun ce akwai yiyuwar abubuwa su kara tsananta idan gwamnati bata dauki matakan da suka dace ba akan lokaci.

Idan ana iya tunawa, a kusan karshen watan Yuni, kamfanonin samar da wutar lantarki na shiya-shiya sun sanar da cewa zasu yi karin kaso 40 cikin 100 na farashin wutar lantarki daga ranar 1 ga watan Yuli, sanarwar da suka janye daga baya, sai kuma sanarwar karshen makon nan da gwamnatin tarayya ta fitar na kari a kań kudin makarantar kwalejojin sakandaren kasar, shima lamarin da masana suka ce ya zo a lokacin da bai kamata ba.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:

Kamata Ya Yi Gwamnati Ta Kawo Tsari Da Zai Amfani Dukka ‘Yan Najeriya - Masana.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:55 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG