ABUJA, NIGERIA - Sun dai bukaci shugaban da ya maida hankali ne ta hanyoyin da suka dace tare da zakulo amintattun mutane da za su jagoranci aikin don ya kai ga mabukata na asali.
Manjo Janar Patrick Adamu Akpa, ya ce cire tallafinn man fetur ya jefa Najeriya cikin rudani da talauci wanda ya shafi kowa kuma kamata ya yi gwamnati ta yi duk mai yiyuwa wajen kawo wa talaka sauki.
Dattawan karkashin Northern Alliance Committee dai sun yi wannan kira ne a daidai lokacin da akasarin ‘yan Najeriya ke kokawa a kan yadda yunwa ke yin sanadiyar mutuwar mutane musamman a yankunan karkara sakamakon tashin farashin kayayyakin abinci bayan cire tallafin man fetur da sabuwar Gwamnati ta yi a karshen watan Mayun.
Ambassada Lawal Muhammad Munir shugaban kungiyar ta Northern Alliance ya bayyana cewa kamata ya yi Gwamnatin tarayyar Najeriya ta mayar da hankali sossai wajen tsara fitar da tallafin rage radadin cire tallafin man fetur ta bangaren zakulo amintattun mutane da za su jagoranci aikin ta yadda za’a samo yadda za’a rage farashin kowacce litar mai, da kuma kawo sauki a fannin kayan abince, ya kara da cewa da zarar an fara samun wadannan abubuwan, to za a samu sauki.
Daraktan tsare-tsare da wayar da kan al’umma a kungiyar Northern Alliance, Alhaji Ibrahim Marmara, ya ce a dakika akwai mawuyacin halin da alumna suka samu kan su a yanzu saboda zancen janye tallafin man fetur, amma in har za’a yi amfani da abun da za’a rika samu daga janye tallafin yadda ya kamata, Najeriya zata ci gaba, ya na mai yin kira ga ‘yan kasa da su dada yin hakuri domin idan gyara za’a yi sai an samu takura.
A bangaren wakilin Arewa maso Gabas na Kungiyar Northern Alliance, Injiniya Saidu Jidda, cewa ya yi yankinsa na cikin matukar tsadar rayuwa amma tun da Gwamnati ba mutum daya ke jagorantar ta ba, dole ne dukkan masu ruwa da tsaki su tashi tsaye wajen sa ido a kan yadda Gwamnatoci a matakan jihohi suna amfani da kudadden da suke samu daga asusun FAAC da ake rabawa duk wata a hanyoyin da suka dace.
Shi ma Malam Sanusi Abbas Sanusi daga yankin Arewa maso Yamma ya ce kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali ta kara duba harkokin noma, ilimi da kuma wutan lantarki don kawo sauki ga al’umma a cikin yanayin da ake ciki
Tun bayan cire tallafin man fetur dai a watan Mayu, masana tattalin arziki sun yi ta jadada mahimmancin gwamnati ta sake daura damarar duba fannoni da dama da zasu bunkasa tattalin arzikin kasar, kamar sake nazari a kan mafi karancin albashi da kuma samar da abubuwan jin ‘kai ga masu karamin karfi a kasar.
Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf:
Dandalin Mu Tattauna