Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CBN Ya Kara Kudin Ruwa Da Maki 25


Banban Bankin Najeriya CBN
Banban Bankin Najeriya CBN

Babban bankin Najeriya wato CBN ya kara kudin ruwa da maki 25 na kaso 1 bisa 100 wanda ke nufin an yi karin daga kaso 18 da digo 5 zuwa kaso 18 da digo 75 cikin 100.

Mukaddashin gwamnan CBN, Folashodun Shonubi, ne ya bayyana hakan a ranar Talata bayan taron kwamitin kula da manufofin kudi na bankin wato MPC da ya gudana a birnin Abuja yana mai cewa kwamitin ya mayar da hankali ne kan yanayin hauhawar farashin kayayyaki da kuma illar da zai iya ci gaba da jawo wa a fannin tsadar kayayyakin masarufi da tasgaro a samun kudin shiga na cikin gida.

Folashodun Shonubi
Folashodun Shonubi

A takaice Fashodu ya ce kwamitin manufofin kuɗi ya yanke shawara kara kudin ruwa da maki 25 tare da amincewar mambobinsa mafi rinjaye don samun ci gaban darajar manufofin kuɗin Najeriya, wanda a taƙaice kudin ruwa ya tashi daga kaso 18.5 zuwa 18.75 cikin 100.

Daya daga cikin mambobin kwamitin manufofin kudi na bankin CBN, Farfesa Aliyu Rafindadi Sanusi, ya yi karin bayani a kan ababen da kwamitin MPC ya cimma a yayin taron su na wannan karo da suka hada da yin kari a kan kudin ruwa, samo dabarun rage hauhawan farashin kayayyaki, jawo hankulan masu zuba jari daga wajen kasar, jawo hankalin yan Najeriya mazauna kasashen waje su rika zuba jari a cikin gida don daidaita tattalin arzikin kasar.

Shonubi da wasu mambobin MPC
Shonubi da wasu mambobin MPC

A wani bangare kuma babban jami’in a bankin CBN, Mal. Haruna Mustapha, ya yi bayani a kan yadda babban bankin ke sanya ido a kan tsare-tsaren sa kan masu sana’ar POS don gujewa cutar al’umma da caji ba bisa ka’ida ba da kuma batun karancin sabbin takardun kudi da yan kasa ke kokawa a kai yana mai cewa, a hankali- a hankali sabbin takardun kudin zasu yawaita kuma bankin CBN ba zai tsawalla batun janye tsaffin takardun kudi daga cikin kasar ba illa ya bari a ci gaba da sakin sabbi don tsoffafin su kare a hankali daga zirga-zirga a hannun jama’a.

Matakin da taron kwamitin MPC ya cimma a wannan karo dai shi ne na farko tun bayan kafa sabuwar gwamnati da shugaba Bola Tinubu ke jagoranta a ranar 29 ga Mayun shekarar 2023.

Kazalika, matakin kwamitin na wannan karon shi ne na farko a cikin kimanin shekaru goma ba tare da gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele wanda shugaba Tinubu ya dakatar a ranar 9 ga watan Yuni, shekarar 2023 da muke ciki.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG