A cewar Nnori, jiragen kasan yanzu za su tashi minti 30 kafin lokacin tashinsu da aka tsara a baya.
Najeriya na sa ran karbar sabbin kayayyakin yaki na jiragen sama 54, da suka hada da jiragen sama na kai hari da jirage masu saukar ungulu da kuma jirage marasa matuka.
Zakarun na 2010 sun gaza cin ko daya daga cikin fenariti da suka buga bayan mintuna 120 da suka buga babu ci a wasansu da Morocco.
Hakazalika, Majalisar ta kuma umarci Gwamnan Babban Bankin na CBN Godwin Emeifele, da ya bayyana a gabanta a ranar Alhamis mai zuwa.
‘Yan majalisar dokokin Birtaniya da Amurka sun yi kira ga gwamantocin kasashensu da su nemi karin bayani daga Najeriya kan rahoton na Reuters.
Masu gabatar da kara a Jamus sun ce wasu jami’ai dubu 3,000 ne suka gudanar da bincike a wurare 130 a jihohi 11.
Wani kudurin doka da zai bada dama a kafa wata Cibiyar horar da 'yan sanda na musamman ya tsallaka karatu na biyu a Majalisar Dattawan Najeriya.
A wannan makon, shirin Lafiyarmu zai maida hankali ne kan raunukan da ake samu a wasanni da kuma yadda za’a iya kare Kai daga samun raunukan yayin da aka fara gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a kasar Qatar.
Kocin Amurka, Gregg Berhalter, ya ce harkar siyasa ba za ta shiga karawar Cin Kofin Duniya da tawagarsa za ta yi da Iran ba, biyo bayan cancaras da aka yi tsakanin Amurka da Ingila ranar Jumma’a.
Breel Embolo ne ya zura kwallo a ragar kasar haihuwarsa da ya baiwa Switzerland nasara da ci 1-0 a kan Kamaru a gasar cin kofin duniya da suka fafata a rukunin G a filin wasa na Al Janoub a yau Alhamis.
A ranar Lahadi 20 ga watan Nuwamba ne za’a soma gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya ta bana a Qatar, karon farko da aka fadada gasar zuwa kasashe 32, haka kuma karon farko a tarihi da za’a gudanar da gasar a yankin kasashen larabawa.
Daraktan Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka FBI, Christopher Wray, ya ce Hukumar FBI na gudanar da bincike kan gudanar da “ofishin ‘yan sanda” ba bisa ka’ida ba da kasar China ke yi a New York na Amurka.
A ranar Lahadi mai zuwa ne za a fara gasar cin kofin duniya ta maza a kasar Qatar, inda magoya baya a Afirka ke sha’awar kallon kungiyoyi biyar na nahiyar da za su fafata a gasar.
Ma’aikatan Majalisar dokokin jihar Taraba sun shiga yaji aikin sakamakon rashi biyansu wasu hakkokinsu na kayan sawa da sauransu har na tsawon shekaru bakwai.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta ce ta shirya tsaf domin dakile halatta kudin haram ta hanyar sayen kaddarori da kayan abinci da tsabar kudi domin kaucewa sabuwar dokar canja Naira.
Jam’iyyar Lebour ta sanar da rasuwar mataimakin shugaban Jam’iyyar na Arewa ta Tsakiya, Adi Shirsha .
Domin Kari