Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar FBI Tana Bincike Bude Ofishin ‘Yan Sandan China A New York


Daraktan Hukumar FBI Christopher Wray (AP Photo)
Daraktan Hukumar FBI Christopher Wray (AP Photo)

Daraktan Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka FBI, Christopher Wray, ya ce Hukumar FBI na gudanar da bincike kan gudanar da “ofishin ‘yan sanda” ba bisa ka’ida ba da kasar China ke yi a New York na Amurka.

Wannan na daya daga cikin iri-irin wadannan ofisoshi da kasar China ke gudanarwa a kasashen duniya, da hukumar ta FBI ta sha alwashin dakatar da ayyukan jami’an tsaron Beijing a Amurka.

Da yake magana yayin da yake bada bahasi gaban kwamitin tsaron cikin gida na Majalisar Dattawa, Wray ya ce hukumar FBI, tana sane da zaman wadannan ofisoshi.”

“Dole ne in yi taka tsantsan game da tattauna takamammen aikin bincikenmu, amma a gare ni, abin ban mamaki ne a yi tunanin cewa ‘yan sandan China za su yi kokarin kafa ofishi a New York, ba tare da tuntuba da ta kamata ba,” in ji darektan FBI.

Aikin na kasar China ya keta 'yancin diyaucin kasa da kuma sabawa tsarin shari’a da na aikin jami’an tsaro”, in ji Wray.

A watan Satumba, kungiyar kare hakkin bil adama da ke kasar Sipaniya mai suna Safeguard Defenders ta ba da rahoton cewa, Sin ta kafa akalla ofisoshin 54 na ‘yan sanda a kasashen waje, a sassan duniya, ciki har da 1 a birnnin New York a Amurka da 3 a Toronto na kasar Canada.

Kungiyar ta ce jerin sunayen nata ya dogara ne akan bayanan hukuma, amma ainihin adadin na iya karuwa.

XS
SM
MD
LG