Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Kwararru Ke Kallon Kudurin Dokar Kafa Cibiyar Horar Da ‘Yan Sanda Ta Musamman A Gwoza


Sanata Mohammed Ali Ndume
Sanata Mohammed Ali Ndume

Wani kudurin doka da zai bada dama a kafa wata Cibiyar horar da 'yan sanda na musamman ya tsallaka karatu na biyu a Majalisar Dattawan Najeriya.

Cibiyar za ta horar da 'yan sandan ne domin su yaki ta'addanci, tada kayar baya, 'yan fashi da makami da sauran munanan laifuka.

Wannan Cibiya da ke garin Gwoza a jihar Borno za ta banbanta da Cibiyoyin horar da 'yan sandan yau da kullum. da ake kira kwalejin 'Yan Sanda.

Ita wannan cibiya ta daban ce wacce za’a inganta ta domin horar da 'yan sanda na musamman, wadanda za su yaki ta'addanci, 'yan fashi da makami, tada kayar baya, da sauran munanan laifuka da ke addabar kasar.

Sanata Mai wakiltan Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume, wanda shine ya kawo kudurin a zauren Majalisar Dattawa, ya bada hujjojin sa yana cewa saukin da ake samu a harkar tsaro a kasar a yanzu saboda ‘yan sanda na musamman din ne.

Ndume ya ce Cibiyar da ke Gwoza ta kwashe shekara 38 tana horar da wani bangare na ‘yan sanda, wanda aka fi sani da ‘yan sandan kwantar da tarzoma, amma yana ganin ya kamata a inganta ta maimakon kai su kasashen waje domin horas da su.

“Ya kamata a ware masu kasafin kudin su, domin su samu yin aiki mai kyau wa kasa,” in ji Ndume.

Mai Sharhi Kan Tsaro, Dr Kabiru Adamu
Mai Sharhi Kan Tsaro, Dr Kabiru Adamu

A nasa bangaren masanin harkar tsaro, Dakta Kabir Adamu, ya bayyana ra’ayinsa a kan yana goyon bayan wannan yunkuri kuma lallai ya kamata a samu irin wannan cibiyar, amma bai kamata a sa har da batun ta'addanci da manyan laifuka a tsarin ba.

Adamu ya ce a kara yunkurin da ake da niyar yi na horar da ‘yan sandan, wajen jawo wasu ababe da ba hurumin su ba ne ba.

Shi ma kwararre a fanin tsaro, Dakta Yahuza Ahmed Getso, ya ce yana ganin wannan ihu ne bayan hari, domin wannan cibiyar ba za ta haifar da da mai ido ba.

Getso ya ce masu fada a ji ne kawai suke so su kawo wata kafa da za su yi amfani da ita wurin daukan 'ya'yan su da ‘yan baranden su aiki, saboda an kwashi shekaru sai maimaita cibiyoyi kawai ake yi a kasar.

Ya kuma bada misalin rundunan SARS da aka kago daga 'yan sandan kasa amma kwaliya ba ta biya kudin sabulu ba.

Shi kuwa mai nazari a fannin zamantakewar dan Adam, Abubakar Aliyu Umar, ya ce a nan din ma wata hanya ce na wawuran kudi, kuma ba ya goyon bayan wannan yunkuri domin kasa ba ta da isassun kudi, basussuka kawai ake ciyowa.

Abubakar ya ce an kwashi shekaru sama da goma sha uku ana fama da harkar tsaro amma ba a kafa irin wannan cibiyar ba sai yanzu.

Majalisar Dattawa ta mika kudurin ga Kwamitin Kula da Harkokin ‘Yan Sanda, inda aka ce ya yi aiki akan kudurin ya dawo da rahoto bayan makonni hudu.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

XS
SM
MD
LG