Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Amince Da Siyo Jiragen Yaki


Jirgin Yakin M-346
Jirgin Yakin M-346

Najeriya na sa ran karbar sabbin kayayyakin yaki na jiragen sama 54, da suka hada da jiragen sama na kai hari da jirage masu saukar ungulu da kuma jirage marasa matuka.

Najeriya ta dauki wannan mataki ne don bunkasa karfinta na yaki da tabarbarewar tsaro a kasar, kamar yadda babban hafsan sojin sama Isiaka Oladayo Amao ya bayyana a ranar Alhamis..

Rikicin mayaka masu da’awar Islama a arewa maso gabas da kuma sace-sacen mutane don neman kudin fansa da wasu ‘yan bindiga a arewa maso yamma, su ne manyan barazanar tsaro ga Najeriya da shugaban kasar na gaba zai fuskanta bayan zaben shugaban kasa da za’a yi a watan Fabarairu mai zuwa.

Amoa ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da aikewa da sojojin saman Najeriya jiragen yaki samfurin m-346, jirage masu saukar ungulu kirar T-129 ATAK, jirage masu saukar unugulu na Agusta 109 Trekker da kuma jirage marasa matuki na Wing Loog II da China ta kera, wadannan na daga cikin kayayyakin yakin sama.

Sai dai bai bayyana ainihin lokacin da za’a kawo wadannan kayayyaki ba, kuma nawa aka biya na kayan ko wacce kasa ko kuma kasashen da aka sayo su.

A bara, Najeriya ta karbi jiragen sama 12 na Super Tucano, shekaru 4 bayan da Amurka ta amince ta sayar ga kasar da ke Yammacin Afirka da jirage masu saukin kai hari domin yaki da masu tayar da kayar baya.

XS
SM
MD
LG