Dubban ‘yan sanda a Jamus sun kai samame a galibin sassan kasar kan wasu da ake zargin masu tsatstsauran ra’yin mazan jiya wadanda ake zargin sun yi yunkurin kifar da gwamnatin kasar.
Jami’an sun ce suna tsare mutum 25.
Masu gabatar da kara na gwamnatin tarayyar Jamus sun ce wasu jami’ai dubu 3,000 ne suka gudanar da bincike a wurare 130 a cikin jihohi 11 daga cikin 16 na Jamus kan masu bin kungiyar da ake kira Reich Citizens.
Wasu mambobin kungiyar sun yi watsi da kundin tsarin mulkin Jamus bayan yakin da kasar ta fuskanta kuma tare da yin kira da a rushe gwamnati.
Ministan Shari’a na kasar Marco Buchmann ya bayyana samamen a matsayin “aikin yaki da ta’addanci,” ya kara da cewa mai yiwuwa wadanda ake zargin sun shirya kai hari da makami a kan ma’aikatun kasar.
Masu gabatar da kara sun ce ana kuma tsare da wasu karin mutane uku ciki har da wani dan kasar Rasha, wadanda ake zargi da goyon bayan kungiyar baya ga mutum 27 da ake bincikensu