Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar FIFA Ta Zargi Kasashen Yamma Da “Munafunci” Kan Gasar Cin Kofin Duniya Ta Qatar 2022


Shugaban FIFA Gianni Infantino
Shugaban FIFA Gianni Infantino

A ranar Lahadi 20 ga watan Nuwamba ne za’a soma gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya ta bana a Qatar, karon farko da aka fadada gasar zuwa kasashe 32, haka kuma karon farko a tarihi da za’a gudanar da gasar a yankin kasashen larabawa.

An kasa kasashen 32 ne zuwa rukuni 8, kasa hudu a kowane rukuni kamar yadda aka al’adanta.

Rukunin A ya kumshi mai masaukin baki wato Qatar, da Ecuador da Senegal da Netherlands.

A rukunin B kuma akwai Ingila da Iran, Amurka da Wales. Sai rukuni C mai kasashen Argentina, Saudi Arabiya, Mexico da Poland.

Kasar Faransa kuma za ta fafata a rukunin D, tare da Australia, da Denmark da Tunisia. A rukunin E kuma kasashen da za su fafata su ne Spain, Costa Rica, Jamus da Japan.

Sai rukunin F kuma akwai kasashen Belgium, Canada, Morocco da Croatia. Rukunin G kuma ya hada hancin kasashen Brazil, Serbia, Switzerland da Kamaru. Yayin da rukuni na karshe wato na H, ya kumshi Portugal, Ghana, Uruguay da Korea ta Kudu.

A daya bangaren kuma hukumar kwallon kafar duniya wato FIFA, ta bayyana kafa wani kwamitin kwararru, domin Nazari tare da ba da bayanai game da dukkanin wasannin da za’a fafata a gasar cin kofin duniya ta bana a Qatar.

A cikin sanarwar da hukumar ta FIFA ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta ce hakan zai kara inganta fahimtar wasan kwallon kafa da kuma gasar a fadin duniya.

Sanarwar ta ce kwamitin zai kasance ne a karkashin jagorancin shugaban sashen bunkasa wasannin kwallon kafa na hukumar ta FIFA Arsene Wenger, tare da sauran membobi da suka hada da Jurgen Klinsmann daga kasar Jamus, da Alberto Zaccheroni daga Italiya, sai Cha Du-Ri daga kasar Korea.

Sauran membobin sune Sunday Oliseh daga Najeriya, da Faryd Mondragon daga Colombia, da kuma Pascal Zuberbuhler daga Switzerland.

Sanarwar ta ci gaba da cewa a lokacin gasar FIFA za ta samar da sahihan bayanai da kididdiga ta zamani da ba’a taba gani ko ji ba a tarihin gasar, ta hanyar dimbin masu kallo da saurare a fadin duniya, kazalika da kuma kasashen da suke fafatawa a gasar da ‘yan wasansu.

A wani labarin kuma shugaban hukumar kwallon duniya ta FIFA, Gianni Infantino, ya zargi kasashen yammaci da kitsa munafunci, a cikin rahoton da suka fitar kan bayanan take hakkin bil adama na Qatar, a jajibirin soma gasar.

A wani taron manema labarai da ba saban ba a Doha, Infantino ya kwashe tsawon kusan sa’a guda yana kariya ga kasar Qatar da kuma gasar ta bana bisa zarge-zargen.

Gasar ta cin kofin duniya ta bana a Qatar dai tana tattare da cece-kuce, da suka hada da mutuwar ma’aikata bakin haure, da kuma muzgunawa wasunsu.

A cikin watan Fabrairun shekara ta 2021, jaridar Guardian ta ruwaito cewa ma’aikata bakin haure dubu 6 da 500 daga Indiya, Pakistan, Nepal, Bangladash da Sri Lanka, sun mutu a Qatar, tun daga lokacin da ta yi nasarar samun damar karbar bakuncin gasar.

To sai dai Infantino ya ce kamata yayi kasashen Turai su nemi afuwa kan abin da su suka aikata a cikin nasu tarihin, a maimakon mai da hankali kan ma’aikata bakin haure a Qatar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG