Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gasar Cin Kofin Duniya: Kamaru Ta Sha Ci Daya Mai Ban Haushi A Hannun Switzerland A Qatar


'Yan wasan Kamaru lokacin da suke atisye a Qatar 2022 (Hoto: Cameroon FA)
'Yan wasan Kamaru lokacin da suke atisye a Qatar 2022 (Hoto: Cameroon FA)

Breel Embolo ne ya zura kwallo a ragar kasar haihuwarsa da ya baiwa Switzerland nasara da ci 1-0 a kan Kamaru a gasar cin kofin duniya da suka fafata a rukunin G a filin wasa na Al Janoub a yau Alhamis.

Embolo ya jefa kwallo gida da dan karami kurosin daga Xherdan Shaqiri bayan mintuna 48, sannan ya tsaya cak tare da murtike fuskarsa yayin da abokan wasansa suka yi murna a kusa da shi. An haifi matashin mai shekaru 25 a Yaounde amma ya girma a Basel.

'Yan wasan Switzerland a gasar nahiyar turai a 2020
'Yan wasan Switzerland a gasar nahiyar turai a 2020

Kamaru ce ta fi buga kwallo mai kyau a zagayen farko kuma watakila da ita zata fara zura kwallo ce kamar yadda Karl Toko Ekambi da Eric Mazima Choupo-Moting da Martin Hangla suka zubar da damarmaki masu kyau a wasan da bangare Switzerland ya yi fama a zagayen farko.

Sai dai ‘yan wasan Switzdrland sun kara kwazo a zagaye na biyu kuma sun kai ga cin kwallo ta hannu Embolo. Rubin Vargas ya barar da wata kaykkaywar dama ta cin kwallo ta biyu amma mai tsaron raga Andre Onana ya ture kwallon yayin da Kamaru ta rasa karsashi.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG