Hukumar Kula Da Zirga-Zirgar Jiragen Kasan Najeriya NRC ta sanar da gyara jadawalin lokacin tashin jiragenta biyu na karshe daga Idu (Abuja) zuwa Rigasa (Kaduna) da kuma wanda zai koma.
Mista Pascal Nnorli, Manajan Jirgin Kasan Abuja zuwa Kaduna (AKTS), ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a yau Juma’a cewa an yi gyare-gyare ne domin tabbatar da isowar jiragen da wuri.
A cewar Nnori, jiragen kasan yanzu za su tashi minti 30 kafin lokacin tashinsu na baya.
“Jirigin AK3 daga Idu (Abuja) da ke tashi da karfe 3:30 na rana don isa Rigasa (Kaduna) da karfe 5:38 na yamma, yanzu zai tashi da karfe 3:00 na yamma, don isa da karfe 5:08 na yamma.” Ya ce
Haka kuma jirgin KA4 na karfe 2:00 na rana daga Rigasa (Kaduna) zai tashi daga Rigasa da karfe 1:30 na rana kuma ya isa Idu (Abuja) da karfe 3:37 na rana, maimakon karfe 4:07 na yamma.
A cewar manajan, gyare-gyaran za su fara aiki ne daga ranar 12 ga watan Disambar, 2022.
Nnorli duk da haka, ya nanata alkawarin kamfanin na tabbatar da kula da tsaron lafiyar fasinjojinsa da kadarorirnsu a cikin jirgensa a kowane lokaci.
Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito cewa hukumar ta NRC ta koma aikin jigilar fasijoji daga Abuja zuwa Kaduna a ranar 5 ga watan Disamba, bayan shafe sama da watanni takwas ba ya aiki.