Tawagar ‘yan wasan La Roja ta fice daga gasar cin kofin duniya a ranar Talata 6 ga watan Disamba, bayan da ta sha kaye a bugun fenareti a hannun Morocco a Qatar.
Zakarun na 2010 sun gaza cin ko daya daga cikin fenariti da suka buga bayan mintuna 120 da suka buga babu ci a wasansu da Morocco.
Sakamakon ban mamaki ya biyo bayan fafatawar da aka yi mai zafi a matakin rukuni, inda ta yi nasara a kan Costa Rica da ci 7-0, kuma ta yi kunnen doki da 1-1 da Jamus, sannan Japan ta doke ta da ci 2-1, wanda hakan ya sa ta zama ta biyu a rukunin E.
Sanarwar da Hukumar Kwallon Kafa ta Masarautar (RFEF) ta fitar ta ce: "Hukumar RFEF na son gode wa Luis Enrique da daukacin jami'an horar da 'yan wasansa da suka jagoranci tawagar kasar a shekarun baya bayan nan.
Hukumar wasanni ta RFEF, sun mika wa shugaban kasa rahoton da aka yanke cewa ya kamata a fara wani sabon aiki ga kungiyar kwallon kafa ta Sifaniya.
Manufar ita ce a ci gaba da daurawa akan ci gaban da aka samu a shekarun baya-bayan nan albarkacin aikin da Luis Enrique da abokan aikinsa suka yi.
Shugaban kasa, Luis Rubiales, da daraktan wasanni, Jose Francisco Molina, sun mika hukuncin ga kocin.