Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Yi Watsi Da Rahoton ‘Zubar Da Ciki’ Da Reuters Ya Fitar


Janar Lucky Irabor (Twitter/@DefenceInfoNG)
Janar Lucky Irabor (Twitter/@DefenceInfoNG)

‘Yan majalisar dokokin Birtaniya da Amurka sun yi kira ga gwamantocin kasashensu da su nemi karin bayani daga Najeriya kan rahoton na Reuters.

Shugaban hafsoshin sojin Najeriya, Janar Lucky Irabor, ya fada a ranar Alhamis 8 ga watan Disamba cewa, rundunar sojojin kasar ba za ta binciki rahoton kamfanin dillanci labarai na Reuters da ke cewa tana gudanar da wani shiri na zubar da ciki a asirce ba saboda rahoton ba gaskiya ba ne.

Kamfanin dillanci labaran Reuters ya ruwaito a ranar Laraba cewa sojojin Najeriya na gudanar da wani shiri na zubar da ciki da ba bisa ka’ida ba a asirce a yankin arewa maso gabashin kasar tun daga 2013.

Shirin ya kunshi zubar da ciki akalla dubu 10,00 a tsakanin mata da yan mata, wadanda da yawa daga cikinsu mayakan masu ikirarin jihadi ne suka yi garkuwa da su tare da yi musu fyade, kamar yadda wasu tarin shaidu da takardu da kamfanin dillanci labaran Reuters ya gani suka nuna.

Da aka tambaye shi game da rahoton, Irabor ya shaida wa manema labarai a Abuja cewa “sojoji ba za su binciki abin da kuka san ba gaskiya ba ne.”

“Ban yi tsammanin ya kamata mu bata lokacinmu a irin wadannan abubuwa ba,” ya bayyana haka yayin da yake magana a wani taron manema labarai da ya yi bayani kan tashe-tashen hankula, ta’addanci, da ‘yan fashin daji.

Irabor, wanda ya jagoranci rundunar soji a yankin arewa maso gabas a shekarar 2016, wani lokaci da rahoton ya bayyana, ya ce wannan al’amari da suke fada a ciki rahoton bai taba faruwa ba, sannan bai taba ganin wani abu makamancin haka ba.

Tun bayan fitar rahoton, kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su gudanar da bincike, da gurfanar da wadanda aka samu da laifi tare da bayar da diyya ga wadanda abin ya shafa.

‘Yan majalisar dokokin Birtaniya da Amurka sun yi kira ga gwamantocin kasashensu da su nemi karin bayani daga Najeriya.

XS
SM
MD
LG