Gabanin zaben cike gurbi da za a yi a gobe Asabar a rumfuna 2,660 a fadin Najeriya, Sufeto Janar na yan sandan, Usman Baba Alkali ya ba wa masu kada kuri’a tabbacin kare lafiyarsu a rumfunan zabe.
Rundunar sojin Sudan ta yi gargadi a jiya Alhamis kan yiwuwar barkewar arangama da dakarun sa kai na kasar masu karfi, wadanda ta ce an girke su tura a Khartuom, babban birnin kasar da sauran wasu yankun ba tare da amincewar sojoji ba.
Mutane biyu ne suka mutu yayin da sama da miliyan guda suka rasa wutar lantarki a ranar Alhamis, bayan da dusar kankara ta afka wa larduna biyu mafi yawan jama’a a kasar Canada, gabanin hutun karshen mako.
Malaman Islama da addinin Kiristan nan biyu wato Imam Nuraini Ashafa da Pastor James Wuye sun nuna cewa hadin kan jama’a ta hanyar kauce wa bambance-bambance ne zai dawo da Najeriya kan turba mai kyau ta zaman lafiya.
Dallar Amurka miliyan 800 da Bankin Duniya ya ba Najeriya domin ta cire tallafin man fetur a tsakiyar wannan shekara, ya jawo cece-kuce tsakanin masana tattalin arziki da masu ruwa da tsaki a kasar.
Mataimakin shugaban babbar jam’iyyar adawar Najeriya PDP Umar Iliya Damagun ya zama mukaddashin shugaban jam’iyyar bayan saukar wucin gadi da shugaban ta Iyorchia Ayu ya yi sakamakon umurnin babbar kotun jihar Binuwai.
A wani bangare na ziyarar aiki na kwanaki uku a Ghana, mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris, ta ziyarci sansanin ajiye bayi mai tarihi dake birnin Cape Coast.
Kwamitin majalisar wakilan Najeriya ya yi zama inda ya karbi shawarwarin jama’a kan kudurin kafa hukumar kula da almajirai da ke ragaita kan tituna musamman na arewacin Najeriya.
‘Yan gudun hijira a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya sun koka akan rashin samun kayan abinci a sansanin ‘yan gudun hijira da ke karamar hukumar Fufore.
Kungiyar Super Eagle ta Najeriya ta farfado inda ta rama ci 1-0 mai ban haushi da Guinea-Bissau ta yi mata a ranar Litinin.
A ranar Talata ne jagororin manyan jami’iyyun adawa a Najeriya biyu suka shigar da kara a kan neman soke sakamakon zaben shugaban kasa na watan Fabrairu da suke kalubalanta, kamar yadda takardun kotu su ka nuna, domin fara wata shari’ar da ka iya daukar tsawon watanni.
Yayin da al'ummar Musulmi a wasu kasashen duniya ke dakon soma azumi, a Najeriya ma yau ne ake soma dubin watan na Ramadan.
Shugaban babban bankin Najeriya wato CBN ya bayyana cewa, kwamitin manufofin kudin bankin ya kada kuri’ar kara yawan kudin ruwa da maki 50 zuwa kaso 18 cikin 100 daga kaso 17 da digo 5 cikin 100.
Domin Kari