Wannan dai dambarwar bayan babban zabe ce tsakanin Ayu da gwamnan jihar Binuwai mai barin gado Samuel Otom.
PDP dai, bayan nazartar umurnmin babbar kotun jihar Binuwai daga Alkali W. I. Kpochi kan dakatar da shugaban jam’iyyar Ayu har sai an kammala sauraron karar da wani dan jam’iyyar mai suna Terhide Utaan ya shigar, ta nada mataimakin shugaban jam’iyyar na arewa, Umar Damagun ya yi jagoranci har kafin mataki na gaba.
Gabanin wannan matsaya, PDP ta mika gwamna Otom ga kwamitin ladabtarwa don rawar da ya taka ta kin marawa dan takarar jam’iyyar a zaben shugaban kasa Atiku Abubakar, inda ya zabi Peter Obi na Leba; don ramawa kura aniyar ta, ta sa mazabar Ayu a Gboko jihar Binuwai ta dakatar da shi don zargin yaki taimakon jam’iyyar a zaben gwamna da hakan ya sa ta fadi warwas APC ta samu nasara.
Kakakin Ayu, Yusuf Dingyadi ya ce jam’iyyar ta yi watsi da dakatarwar mazaba da nuna sam mazabar ba ta da wannan hurumi amma a yanzu Ayu ya zakuda don bin umurnin shari’a.
Manyan ‘yan PDP irinsu Dahiru Bobbo na cewa duk da rashin mara bayan Otom da ‘yan tawagar bara’a karkashin Wike, dan takarar PDP Atiku ne ya ke da tsarin hada kan ‘yan kasa da samun karbuwa a kowane bangare.
PDP ta sa bulalarta ta dakatar da manyan ‘yan jam’iyyar irin su Anyim Pious Anyim, Chimaroke Nnamani, Ayo Fayose, Ibrahim Shema don samun su da laifin angulu da kan zabo.
Shin PDP za ta murmure daga wannan tsama da ke tsakanin manyan ‘ya’yanta? Atiku dai na kotu don bukatar a yi watsi da ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban Najeriya.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya: