Bayan an zagaya da ita cikin ginin, ta fito cike da hawaye, ta yi jawabi kan laifukan da suka faru a sansanin da ya kasance cibiyar cinikin bayi a zamanin mulkin mallaka.
Mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris, muryarta na rawa yayin da take kwatanta abin da ta gani a cikin sansanin ajiye bayin bayan ta fito daga sansanin.
Tace, “Tilas ne a tuna da firgicin abin da ya faru a nan. Ba za a iya hanawa ba. Tilas ne a koyar da shi; Tilas ne a koyi tarihi”.
Yayin da ake zagaya da Kamala Harris da maigidanta, Doug Emhoff, tana yawan girgiza kanta saboda yadda aka musguna wa bayi a daidai wurin da suke tafiya.
Akwai lokacin da Harris ta dan tsaya ta goge hancinta ta shaki iska, musamman lokacin da aka nuna mata kurkukun bayi mata.
Ta kara da cewa: “An sace su daga gidansu. Aka kwashe daruruwan mil ana tafiya da su, ba su da tabbacin inda suka dosa. Sai suka zo wannan wurin mai ban tsoro”. Wasu sun mutu, da yawa kuma sun ji yunwa kuma aka azabtar da su. An yi wa wasu mata fyade kafin a yi tafiya da su na dubban mil daga gidansu domin a sayar da su ga wasu da ake kira ’yan kasuwa. A kai su Amurka zuwa Karebiyan don su zama bayi.”
Shin ko me mataimakiyar shugaba Kamala Harris ta gani ya jijjiga ta haka? Tambayar da na yi wa Malam Abubakar Garba Osuman, dan jarida kuma masanin tarihi kenan. Ya ce, duk wanda ya shiga cikin ginin, tilas ne ya tausaya, domin yadda aka tsara wajen; a cikin akwai wani kurkuku da ake cewa ‘Dungeon’ a turance, wanda yake mutum bai ganin dan’uwansa saboda duhun wurin.
Ya kara da cewa, wurin da ake cewa “Point of no return”, wato inda ba a dawowa; daga wurin sai teku, ko bayin su shiga cikin jirgin ruwa ko kuma a jefa shi teku.
Uwargida Kamala Harris ba ta kawo batun diyya ga kasashen da aka kwashe jama’arsu zuwa kasashen waje domin cinikin bayi ba.
Sakataren jam’iyar CPP na yankin Ashanti kuma masanin tarihi, Malam Issah Abdul Salam, ya ce Amurka ba ta yi laifin cinikin bayi ba, domin haka, ba lalle ba ne ta yi batun diyya ba.
Amma kasashen Turai, kamar Ingila, Holland, Jamus da sauransu ne suka yi cinikin bayi. Ya ce, idan sun ba da diyya zai rage wani radadin wulakanci da aka yi wa ‘yan Afirka.
Kamala Harris dai, ita ce mataimakiyar shugaban kasar Amurka, bakar fata ta farko, da ta ziyarci wannan sansanin ajiyar bayi na Cape coast.
Saurari rahoton Idris Abdallah Bako: