Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Rundunar Yan Sanda Ta Shirya Wa Zaben Cike Gurbi Na Gobe Asabar


IGP Alkali Baba Usman
IGP Alkali Baba Usman

Gabanin zaben cike gurbi da za a yi a gobe Asabar a rumfuna 2,660 a fadin Najeriya, Sufeto Janar na yan sandan, Usman Baba Alkali ya ba wa masu kada kuri’a tabbacin kare lafiyarsu a rumfunan zabe.

Ya kuma ba da umarnin tura ‘yan sanda zuwa kananan hukumomi 185 a fadin jihohi 24 na tarayyar kasar, inda za a sake gudanar da zabe a ranar Asabar.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a Najeriya (INEC) a lokacin zabukan ranar 25 ga watan Fabrairu da 18 ga watan Maris ta bayyana wasu zabukan gwamnoni, da na ‘yan majalisun tarayya da na jihohi da ba su kammala ba tare da bada umarnin sake zaben.

Tashen tashen hankula da aka samu da hana masu kada kuri’a zabe ya mamaye zabukan 25 ga watan Fabrairu da 18 ga watan Maris, musamman a jihohi kamar Lagos da Rivers, da dai sauransu, yayin da ‘yan daba suka yi ta’addanci kan masu kada kuri’a a rumfunan zabe, lamarin da ya kara rura wutar rashin jin dadin masu zabe.

A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta Najeriya, Muyiwa Adejobi, ya ce shugaban ‘yan sandan ya ba da umarnin aikewa da isassun jami’ai da ke tallafawa da kuma Karin kayan aiki don samar da ingantaccen tsaro a zaben da za’a gudanar a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, 2023.

A wani bangare sanarwa ta kara da cewa, “Karin tallafin ya hada da tura ma’aikata, motocin aiki, makamai da rigunan kare kai da kayan yaki da tarzoma da dai sauransu.

“Hakazalika, Sufeto Janar na yan sandan ya umarci manyan jami’an ‘yan sanda da ke kuda da wasu yankuna inda za a gudanar da zaben, musamman zaben gwamnoni a jihohin Adamawa da Kebbi, da su tabbatar da samar da isasssun ma’aikata da sauran kayakin aiki, domin gudanar da ingantaccen aikin ‘yan sanda a zaben.”

Babban Sufeton ‘yan sandan ya bukaci masu zabe a jihohin da abin ya shafa da su fito sosai domin yin amfani da ikon doka ta basu na zabe da kuma bin doka da oda tare da wanzar da zaman lafiya.

XS
SM
MD
LG