Shugaban ‘yan hijira na sansanin Alhaji Bakura Umar ne ya yi wannan kira. Ya kuma kara da cewa daman wata wata hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya reshen jihar Adamawa ke kawo ma su tallafin a can baya.
Amma yanzu kimanin wata shida zuwa bakwai ke nan ba su samu kowane irin tallafi ba ta kowane bangare.
Ita ma Shugabar mata ta sansanin 'yan gudun hijira na Fufore, Safiratu Ayuba ta ce a gaskiya suna cikin damuwa musamman batun abinci, inda lamarin ya fi kamari tsakanin yara, mata da tsofaffi.
Ta ce a halin yanzu mata sai sun je kalen shinkafa ko masara a jeji kafin su ci abinci, inda hakan ke kokarin gagararsu.
Shi ma wani dattijo da ya shafe sama da shekaru 50 da haihuwa a duniya mai suna Usman Abba ya yi kira da mahukunta da su taimaka musu da abin da za su ci a wanna wata na azumi, inda yanzu suka shafe kusan wata biyar ba a kawo musu abinci ba.
A nasa bangare, shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya reshen jihar Adamawa, Mr. Ladan Ayuba ya ce yanzu haka yana birnin Abuja domin mika wannan korafin na ‘yan gudun hijiran da suke sansanin Fufore kuma yana mai ba su hakuri kuma za a yi kokarin ganin an kawo karshen wannan matsalar.
Saurari cikakken rahoton Lado Salisu Mohammed Garba: