Kwamitin majalisar wakilan Najeriya ya yi zama inda ya karbi shawarwarin jama’a kan kudurin kafa hukumar kula da almajirai da ke ragaita kan tituna musamman na arewacin Najeriya.
‘Yan majalisa 17 su ka dau nauyin kudurin da yin azamar kammala shirya shi don samun amincewar majalisa mai ci ta 9, gabanin kammala aikin ta a watan Yuni mai zuwa.
Mutane daga bangarorin addini, ilimi da kungiyoyin kare hakkokin yara sun gabatar da jawabai da mika takardun mara baya ga kafa hukumar don kula da yaran da ke zama cikin yunwa, rashin muhalli mai kyau da sutura.
Duk da wasu sun soki lamirin kudurin da cewa tamkar ya shafi almajirai Musulmi ne kadai, masu gabatar da kudurin sun ce kowane yaro na da hakkin samun kulawa daga gwamnati don tada shugabannin gobe masu nagarta.
‘Yar majalisar wakilan kuma tsohuwar minista a ma’aikatar ilimi, Aishatu Jibrin Dukku, na cikin na kan gaba a daukar nauyin kudurin da ta ce za su jajirce don ya zama cikin kudurorin karshe da shugaba Buhari zai sanya wa hannu.
Tsohon darakta a fadar Aso Rock, Auwal A. Maidabino, ya karfafa batun dawowa da makarantun tsangaya da a kan hada da karatun zamani a arewacin Najeriya don hakan ya ceto miliyoyin yara daga wahalar rayuwa da su ke shiga don rashin kulawar gwamnati.
Alkaluma dai sun nuna akwai yara kimanin miliyan 13 da ke gararamba a arewacin Najeriya kadai da ke bukatar kulawa ta akalla abinci da muhalli mai kyau.
Masana sun ce rashin daukar nauyin yaran babbar barazana ce da za ta iya yaye wata al’umma a nan gaba da ba tausayi kuma ba sani ba sabo.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikya: