Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Sudan Ta Yi Gagadi Kan Yiwuwar Rikici Ya Barke Bayan Da Kishiyarta Ta Girke Dakaru


Sudan
Sudan

Rundunar sojin Sudan ta yi gargadi a jiya Alhamis kan yiwuwar barkewar arangama da dakarun sa kai na kasar masu karfi, wadanda ta ce an girke su tura a Khartuom, babban birnin kasar da sauran wasu yankun ba tare da amincewar sojoji ba.

A 'yan watannin baya bayan nan dai ana takun saka tsakanin sojoji da yan sa kai na farar hula, da aka fi sani da Rapid Support Forces ko RSF, lamarin da ya tilasta jinkirta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kasashen duniya ke mara wa baya da jam’iyyun siyasa domin komar da kasar kan mulkin dimokaradiyya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojin ta ce jibge dakarun RSF a birnin Khartoum da sauran wurare a kasar an yi shi ne ba tare da amincewa ba, ko kuma hada kai da jagorancin sojoji kuma wannan karara an karya doka.

A baya bayan nan ne rundunar yan sa kai ta tura dakarunta zuwa kusa da garin Merowe na arewacin Sudan. Har ila yau, faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta a ranar Alhamis, sun nuna wasu motoci dauke da makamai na RSF da ake jigilar su zuwa birnin Khartoum, zuwa kudancin kasar.

Tashin hankalin na baya bayan nan tsakanin sojoji da jami’an tsaro ‘yan sa kai ya samo asali ne daga rashin jituwa kan yadda ya kamata a shigar da RSF a cikin sojoji da kuma yadda hukuma ya kamata ta kula da aiki. Hadakar dai wani muhimmin sharadin ne na yarjejeniyar mika mulki Sudan da ba a saka hannu ba.

Hamayya tsakinin sojojin da RSF, ya samo asali ne tun lokacin mulkin shugaba Omar al-bashir, wanda aka hambarar a shekarar 2019.

Karkashin al-Bashir, dakarun ‘yan sa kai da Janar Mohammed Hamdan ke jagoranta, ta samo asali ne daga tsoffin tsagerun da aka fi sani da Janjaweed, wadanda suka kai mummunar farmaki a yakin Darfur na kasar Sudan a tsawon shekaru da dama aka kwashe ana rikici a can.

AP

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG