Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Birtaniya Na Jigilar Masu Neman Mafaka Zuwa Rwanda Ya Janyo Bacin Rai


Firayim Minista Boris Johnson
Firayim Minista Boris Johnson

Gwamnatin Birtaniya ta kulla yarjejeniya da kasar Rwanda domin aikewa da wasu masu neman mafaka zuwa kasar dake gabashin Afirka, matakin da 'yan siyasa masu adawa da 'yan gudun hijira suka yi Allah wadai da shi.

Sakatariyar harkokin cikin gida Priti Patel ta ziyarci Kigali babban birnin kasar Rwanda a ranar Alhamis domin rattaba hannu kan abin da kasashen biyu suka kira kawancen bunkasa tattalin arziki.

Shirin zai tursasa wasu mutanen da suka isa Birtaniya a cikin matattarar manyan motoci ko kuma cikin kananan kwale-kwale zuwa Rwanda har abada.

Wasu 'yan gudun hijira
Wasu 'yan gudun hijira

Baƙi sun daɗe suna amfani da arewacin Faransa a matsayin hanyar isa Birtaniyya, ko kuma ta ɓoyayyiyar hanya cikin manyan motoci ko jiragen ruwa.

Lamarin da ya ci gaba da karuwa tun lokacin da annobar aCOVID-19 ta yi sanadiyar rufe wasu hanyoyin a cikin 2020.

Firayim Minista Boris Johnson ya fada a ranar Alhamis cewa ana bukatar daukar matakin ne don dakatar da "mugayen masu safarar mutane wadanda ke cin zarafin masu rauni yayin da suka mayar da tashar ta zama makabarta ruwa."

A cikin wani jawabi da ya yi kusa da gabar tekun Channel, Johnson ya ce "duk wanda ya shiga Birtaniya ba bisa ka'ida ba ... za a iya ƙaurar da shi zuwa Rwanda yanzu."

Gwamnatin Rwanda ta ce Birtaniyya ta biya Fam miliyan 120 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 158 don biyan kudin gidajen bakin hauren.

Ya ce za a ba su "yawan damammaki don gina ingantacciyar rayuwa a cikin ƙasar da ta kasance a koyaushe a matsayin ɗaya daga cikin mafi kwanciyar hankali a duniya."

Johnson ya musanta cewa matakin na "rashin tausayi ne" amma ya yarda cewa matakin zai fuskanci kalubalen doka kuma ba zai fara aiki nan take ba.

Irin wadannan manufofin da aka gabatar a da na tura masu neman 'yan gudun hijira zuwa kasashen waje sun yi sandiyar tashe-tashen hankalula sosai.

A cikin 2013, Australia ta aika masu neman mafaka da ke ƙoƙarin isa ƙasar ta jirgin ruwa zuwa Papua New Guinea da kuma Nauru, tare da cewa ba za a bar kowa ya zauna a Australia ba.

Isra'ila ta aika da mutane dubu da dama zuwa Rwanda da Uganda a karkashin wani tsari na “tafi da son ranka" da aka gudanar a sirrance tsakanin 2014 da 2017.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya caccaki al’ummar duniya kan manufofin musamman mayar da hankali kan yakin da ake yi a kasar Ukraine, yana mai cewa ba a ba da la’akari da rikice-rikice a wasu kasashe be ciki har da kasarsa ta Habasha, watakila saboda wadanda ke fama da matsalar ba fararen fata ba ne.

Shi ma Shugaban Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira da ke zaune a Burtaniya, Enver Solomon, ya kira shirin "mummunar shawara"

Sabon kudirin na gwamnatin ta Johnson da ta bullo mai tsauri na shige da fice zai zamane mai wahala ga mutanen da suka shiga kasar ta hanyoyin da ba su ba da izini ba don neman mafaka kuma zai ba da damar tantance masu neman mafaka a kasashen waje. Ya zuwa yanzu dai majalisar ba ta amince da shi ba.

~ AP

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG