Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Yi Kidayar Jama'a A Badi


Unguwar Oyingbo a jihar Legas (Reuters)
Unguwar Oyingbo a jihar Legas (Reuters)

Tun shekarar da ta gabata  ne Najeriya ta shirya gudanar da kidayar jama’a a amma aka yi watsi da shi saboda karuwar rashin tsaro.

A shekara mai zuwa ne Najeriya za ta gudanar da kidayar jama'arta na farko cikin shekaru 17, domin kokarin tantance yawan al'ummarta, wanda aka kiyasta sama da mutane miliyan 200 kuma mafi girma a Afirka, in ji shugaban hukumar kula da yawan jama'a ta kasar a ranar Alhamis.

Kidayar jama’a a Najeriya a ko da yaushe, kan haifar da ce-ce-ku-ce domin a baya kungiyoyin kabilu da addinai masu adawa da juna sun yi kokarin amfani da su wajen tabbatar da fifikonsu na lambobi da kuma daukar kaso mai tsoka na kudaden shigar man fetur da kuma wakilcin siyasa.

Tun shekarar da ta gabata ne Najeriya ta shirya gudanar da kidayar jama’a a amma aka yi watsi da shi saboda karuwar rashin tsaro, musamman a arewacin kasar da ake fama da tashe-tashen hankula na ‘yan bidiga da kuma sace-sacen mutane domin neman kudin fansa.

Matsalar tsaro dai na ci gaba da zama kalubale yayin da ‘yan bindiga ke kara kai hare-hare da yin garkuwa da mutane, inda ko a ranar Lahadin da ta gabata din nan an kashe mutane 154 tare da yin garkuwa da wasu da dama a wani hari da aka kai a jihar Filato da ke arewacin kasar.

Al’ummar Najeriya sun rabu ne tsakanin Musulmi a Arewa da Kirista a Kudu, da kuma tsakanin kabilu 300.

Bankin Duniya ya kiyasta yawan mutanen Najeriya zai zarce na Amurka nan da shekarar 2050 zuwa kusan miliyan 400.

~ REUTERS

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG