Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bakin Haure Sama Da 90 Sun Nitse A Tekun Bahar Rum – Kungiyar Likitocin Doctors Without Borders


Mutane fiye da 90 da ke cikin wani kwale-kwale mai cunkoso sun nitse a tekun Bahar Rum, a wani sabon bala'i da ya shafi bakin haure da su ka taso daga arewacin Afirka don neman ingantacciyar rayuwa a Turai a cewar kungiyar likitocin agaji ta Doctors Without Borders (MSF).

Kungiyar ta MSF ta fadi da yammacin jiya Asabar cewa bakin hauren na cikin wani jirgin ruwa ne da ya taso daga Libya a makon jiya. Ba a dai san takamaiman lokacin da jirgin ya shiga cikin matsala ba, in ji Juan Matias Gil, shugaban tawagar kungiyar.

Kungiyar wacce kuma aka fi sani da MSF a faransanci, ta ce wani jirgin ruwan dakon mai ya kubutar da wasu bakin haure hudu da sanyin safiyar Asabar a yankin ruwan kasa da kasa. Wadanda suka tsira sun ruwaito cewa suna cikin jirgin tare da wasu bakin haure kusan 100, in ji kungiyar.

MSF ta ce jirgin ruwan man ba ya amsa kiran da ta yi na kar a mayar da bakin hauren zuwa Libya ba, inda "kusan ba makawa za su fuskanci tsarewa, cin zarafi da kuma musgunawa."

Kungiyar ta bukaci Italiya da Malta da su sanya wa wadanda suka tsira wurin mafaka kafin lokaci ya kure. Har ila yau, ta yi kira ga hukumar kare iyakokin Tarayyar Turai Frontex da sauran hukumomin EU su bayyana cikakkun bayanai game da lamarin.

'Yan ci-rani a kai a kai sukan yi kokarin tsallakawa tekun Bahar Rum daga kasar Afurka ta Arewa a wani yunkuri na neman isa gabar tekun Turai. Kasar ta zama babbar hanyar safarar bakin haure da ke guje wa yaki da fatara a Afurka da Gabas ta Tsakiya.

Masu fataucin bil adama a shekarun baya-bayan nan sun ci gajiyar rudamin da ke faruwa a kasar Libya, inda suke safarar bakin haure ta kan iyakokin kasar mai arzikin man fetur da ke da dogon kan iyaka da kasashe shida. Sannan yawanci bakin hauren na cushewa cikin kwale-kwalen roba marasa kayan aiki kuma suna tafiya cikin teku mai hatsari.

Kimanin bakin haure 300 ne suka mutu ko kuma aka yi zaton sun mutu a hanyar tsakiyar Bahar Rum tsakanin 1 ga watan Janairu zuwa 28 ga Maris, a cewar Hukumar Kula da Hijira ta Duniya. Kimanin 3,100 ne aka kama aka kuma mayar da su Libya.

Da zarar sun koma Libya, yawanci ana kai bakin hauren zuwa cibiyoyin tsare mutane na gwamnati da ke cike da cin zarafi da musgunawa.

A 2021, aƙalla bakin haure 32,425 aka kama aka dawo da su Libya. Akalla mutane 1,553 ake kyautata zaton sun nitse a bara, a cewar IOM.

Masu binciken da babbar hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar, sun gano wasu shaidun da ke nuna yiwuwar aikata laifukan cin zarafin bil'adama a Libya kan 'yan ciranin da ake tsare da su a kasar.

~ AP

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG