Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Allah wadai Da Harin Da Aka Kai Kan Jirgin Kasa A Najeriya


General Antonio Guterres
General Antonio Guterres

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi kakkausar suka kan harin da aka kai filin jirgin saman Kaduna da kuma jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna a ranakun 26 da 28 ga watan Maris, wanda rahotanni suka ce an kashe mutane da dama, ko jikkata, ko kuma sace su.

Babban sakataren ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, ya kuma yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata, tare da yin kira da a gaggauta sakin wadanda aka sace.

Babban sakataren ya bukaci hukumomin Najeriya da kada su yi kasa a gwiwa wajen gurfanar da wadanda ke da alhakin wadannan laifuka a gaban kuliya.

Ya kuma jaddada goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ga gwamnati da al’ummar Najeriya a yakin da suke yi da ta’addanci da masu tsatsauran ra’ayi da ma masu aikata muggan laifuka.

A daren ranar Litinin ne 'yan bindiga suka far wa jirgin kasan yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, babban birnin kasar.

Wannan ba shi ne karo na farko da maharan suke kai farmaki kan jirgin ba, a 'yan watannin baya sun taba fasa hanyar layin dogon, ko da yake ba su yi nasarar kama kowa ba.

Sai dai a wannan karon, rahotanni sun ce akalla mutum bakwai sun mutu yayin da wasu suka jikkata kana an sace wasu daga cikin su.

Fannin sufurin jirgi da hukumomin Najeriya suka samar daga Abuja zuwa Kaduna, ya saukakawa mutane da dama wajen yin kasadar bin hanyar mota saboda 'yan fashin daji da ke garkuwa da mutane.

A hali yanzu, hukukumar sufurin jirgin kasar Najeriya ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasar.

XS
SM
MD
LG