Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Amince Da Siyarwa Najeriya Makaman Dala Biliyan Daya


Antony Blinken, Sakataren Harkokin Wajen Amurka
Antony Blinken, Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Gwamnatin Biden ta baiwa Najeriya damar siyan manyan jirage masu saukar ungulu na kai hare-hare na kusan dalar Amurka biliyan 1 duk da damuwar da kasar ke da ita ta zargin take hakkin bil adama yayin da kuma take fama da barazanar kungiyoyin 'yan bindiga da masu tsattsauran ra'ayi a arewacin kasar.

A ranar Alhamis ne ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da amincewa da sayar da dala miliyan 997 na jirage masu saukar ungulu da ake kira Bell AH-1Z Viper guda 24 da makamantansu ga Najeriya.

Kayayyakin sun haɗa da na’urar hangen nesa da daddare da wasu na’urori da injuna da tallafin horo, in ji sanarwar ga Majalisa.

An ci gaba da cinikin ne bayan ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kai Abuja a watan Nuwamba inda ya nuna damuwarsa game da take hakkin bil Adama a Najeriya.

A yayin ziyarar, Blinken ya kuma bayyana cewa, Amurka na daukar Najeriya a matsayin abokiyar kawance wajen yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayin IS a yammacin Afirka da kuma yankin Sahel, yankin da ke gabar hamadar Sahara da ke fadin arewacin Afirka, kuma tana neman kara hadin gwiwa da ita a cikin wadannan yankunan.

An dade ana zargin jami'an tsaron Najeriya da take hakkin bil'adama a ayyukansu.

A watan Oktoban 2020, sojoji sun bude wuta a wata zanga-zanga a cibiyar tattalin arzikin kasar kan daruruwan mutane da ke zanga-zangar nuna rashin amincewa da zaluncin 'yan sanda, inda suka kashe mutane 11 tare da jikkata wasu da dama, a cewar wani kwamitin da gwamnati ke marawa baya.

A ziyarar da Blinken ya kai a watan Nuwamba, ya ce Amurka na fatan ganin cikakken sakamakon binciken kuma za ta yanke shawara kan sayar da makamai ga Najeriya biyo bayan binciken da aka yi na wadanda ke da hannu a lamarin kuma a hukunta su.

Har ila yau Najeriya na fuskantar barazana daga kungiyoyi masu dauke da makamai da kuma 'yan ta’adda masu tsattsauran ra'ayi wadanda a yanzu ke aiki tare a yankin arewa maso yammacin kasar da ke fama da rikici tare da yin barazanar kara dagula al'amura a yankin da ke fama da rikici.

Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a Afirka mai yawan mutane miliyan 206, tana fama da tashe-tashen hankula a arewacin kasar.

~ AP

XS
SM
MD
LG