Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Jajantawa Mutanen Da Hadarin Jirgin Ruwa Ya Rutsa Da Su A Sokoto


Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

Shugaba Buhari ya umarci hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa (NIWA) da ta kara kaimi wajen tabbatar da tsaron tafiye-tafiyen koguna a kasar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi matukar bakin ciki da samun labarin mutuwar mutane 29 a wani mummunan hatsarin jirgin ruwa a kogin Shagari da ke Gidan Magana a karamar hukumar Shagari ta jihar Sokoto.

Gawarwakin Wadanda Suka Rasu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Sokoto
Gawarwakin Wadanda Suka Rasu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Sokoto

Shugaban ya yi wadannan kalamai ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar wacce Muryar Amurka ta sami kwafi inda ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu a wannan mummunan lamari, musamman hakimin Gidan Magana, Malam Muhammadu Auwal, wanda ya rasa ‘ya’yansa biyar a cikin wannan hatsari.

Shugaba Buhari ya umarci hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa (NIWA) da ta kara kaimi wajen tabbatar da tsaron tafiye-tafiyen koguna a kasar.

Buhari ya kuma mika ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar Sakkwato, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma baiwa iyalai da suke makoki hakurin rashi.

Wannan dai ba shi karon farko da ake samun hatsarin kwalekwale a yankin arewa maso yamma da ke Najeriya ba, ko a bara wasu mutane da dama sun mutu sanadiyyar nustewar kwalekwale a jihar Kebbi.

A lokuta da dama hukumomin kan dora alhakin hakan ne akan cunkoso da ake samu a kwalekwale a lokacin da ake safarar mutane.

XS
SM
MD
LG