Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayan Kai Hari Ma Jirgin Kasa a Najeriya, Maharan Sun Tuntubi Iyalai Don Neman Kudin Fansa


'Yan Bindiga
'Yan Bindiga

Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindigar da su ka kai hari ne, sun tuntubi wasu iyalai a Najeriya inda suka ce suna tsare da ‘yan uwansu da suka bace sakamakon harin da aka kai kan wani jirgin kasa a wannan makon, kuma za su bukaci a biya su kudin fansa, a cewar iyalan a ranar Alhamis.

Hukumomi a jihar Kaduna da ke arewacin kasar sun ce mutane takwas ne suka mutu sannan 26 na kwance a asibiti bayan da wani gungun ‘yan bindiga ya tarwatsa hanyar jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna, tare da yin garkuwa da wasu fasinjoji da ba a san adadinsu ba da daren ranar Litinin.

Ibrahim Abba ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa wasu mutanen da ba a san ko su waye ba sun kira iyalansa da yammacin ranar Talata, inda suka sanar da su cewa suna tsare da dan uwansa, wanda ya ce ba a gan shi ba tun bayan harin da aka kai wa jirgin.

“Sun tabbatar mana da cewa yana nan lafiya tare da su.” Inji Abba, ya kara da cewa mutanen sun ce za su dawo da umarnin yadda za a biya su kudin fansa.

Wani dan jaridar Kaduna wanda mahaifiyarsa da ‘yar uwarsa na cikin fasinjojin da suka bata, ya ce ‘yan bindigar da ake zargin, sun tuntube su da daren Laraba.

"Wannan ya ba ni tabbacin da cewa mahaifiyata da 'yar'uwata suna raye, sun ce kasa kunne, za a sake kiranmu kan neman kudin fansa," in ji dan jaridar.

Haka kuma wata mata mai suna Malama Hadiza Goggo ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ita ma ta samu waya da daren ranar Talata kuma an ce mata ta kasa kunne za a tuntube ta da neman kudin fansa na wasu ‘yan uwanta biyu da suka bata.

'Yan bindiga dai sun dade suna kai hare-hare a yankin arewa maso yammacin Najeriya ta hanyar yada ta’addanci a tsakanin al’umma inda suke yin garkuwa da ‘yan makaranta da mazauna kauyuka tare da kai farmaki kan jami’an tsaro.

~ REUTERS

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG