A ‘yan sa’o’i kadan da suka gabata ne aka rika yada fargaba a shafukan sada zumunta kan cewa ‘yan bindiga da sun tare hanyar Kaduna zuwa Abuja tare da yin garkuwa da mutanen da ke kan hanyar.
"Batun da ake yadawa karya ne kuma gungun masu sha'awar yadda labarai marasa dadi a kafofin watsa labarun ne suka yadda su," a cewar wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinan kula da tsaron cikin gida na jihar ta Kaduna, Samuel Aruwan.
Sanarwar ta kara da cewa, bayanan da aka bayar na farko sun nuna cewa ‘yan bindigan ne suke tserewa daga harin da sojoji suke kai musu, yayin da suka yi yunkurin bi ta wata ‘yar karamar hanya a yankin Kasarami a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
"Tuni dakarun suka yi gaggawar zuwa wurin bayan sun sami rahoton leken asiri, inda suka tare su a cikin wani dajin." In Aruwan.
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta sanar da jama'a idan aka sami karin bayani.
"Gwamnatin jihar Kaduna ba ta musanta kasancewar kalubalen tsaro ba, kuma tana ci gaba da yin aiki tukuru tare da jami’an tsaro da sojoji da abin ya shafa." In ji Aruwan.
Wannan na zuwa bayan harin da 'yan bindiga suka kai a daren ranar Litinin inda suka far wa wani jirgin kasa yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, babban birnin kasar.