Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Rukunin Gidajen Masu Karamin Karfi A Kaduna


Jami'in yada labarai da hulda da jama'a na gwamnmatin jihar Kaduna, Samuel Aruwan
Jami'in yada labarai da hulda da jama'a na gwamnmatin jihar Kaduna, Samuel Aruwan

Wasu mahara da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun kai hari a wani rukunin gidajen masu karamin karfi da ke Kofar Gayan a karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna inda suka yi garkuwa da mutane shida da suka hada da wani jami’in Kwastam da dansa.

Har yanzu dai hukumomin ‘yan sanda ba su tabbatar da faruwar lamarin ba, amma majiyoyi da dama na bada rahoton cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan ne da misalin karfe 8 na daren Laraba inda suka fara harbe-harbe kai tsaye yayin da suka kuma shiga gidan wani jami’in kwastam suka wuce da shi tare da dansa.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun bi sawun sa ne daga gidan iyalansa da ke cikin garin Zariya har rukunin gidajen masu karamin karfi. Daga baya ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wasu mutane hudu daga cikin rukunin gidajen masu karamin karfi.

Lamarin dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan wani jirgin kasa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda suka kashe mutane takwas, suka jikkata 26, tare da yin garkuwa da wasu mutanen dahar yanzu ba a tantance adadinsu ba.

Jihar Kaduna dai da wasu jihohi da dama a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya sun sha fama da matsalar ‘yan fashi a shekarun baya.

‘Yan bindigar sun fi kai hari kan makarantu da sauran wuraren jama’a

Duk da kokarin da hukumomin tsaro da gwamnati ke yi, ana ci gaba da kai hare-hare kuma lamarin na cigaba da janyo fargabar al’umma.

Yayin da ‘yan bindigar wadanda tun daga lokacin gwamnati ta ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda, suka fara kai hari a wasu kauyukan da ke wajen jihohin kasar nan, sai da suka yi kaurin suna wajen sake kai farmakin.

A farkon watan ne maharan suka kai hari a filin jirgin Kaduna kafin su mamaye layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna kwanaki kadan, lamarin da ya tilastawa matafiya komowa yin zirga-zirgar ababen hawa da aka yi watsi da su saboda tabarbarewar tsaro a jihar.

XS
SM
MD
LG