Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da akalla mutane 60 a wani yanki mai nisa a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya wadanda galibinsu mata ne masu gudanar da Maulidin Annabi Muhammad, kamar yadda mazauna jihar suka bayyana jiya Alhamis.
Shugabanin kasashe da na gwamnatocin Afrika sun gudanar da taron wuni 1 a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijer.
Saudiyya ta samu gagarumar nasara yau Talata bayan da ta doke Argentina da ci 2-1 a wasansu na farko a gasar cin kofin duniya ta maza a Qatar.
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jagoranci kaddamar da aikin hakar arzikin man fetur na farko a Arewacin Najeriya.
Gwamnatin rikon kwaryar Burkina Faso ta bayyana takaici a game da abinda ta kira halin ko in kular da wasu kasashe abokan kawancenta ke nuna mata dangane da halin tabarbarewar sha’anin tsaron da ta tsinci kanta ciki sakamakon aika - aikar ‘yan ta’adda yau shekaru a kalla 7.
Madugun kamfen din samun tikitin dan takarar APC Bola Tinubu, Babachir David Lawan ya fito karara ya ce bai ga yadda Tinubu zai lashe zaben 2023 ba tun da bai dauki kirista mataimaki ba.
Kungiyar kwallon kafa ta kasar Netherlands ta doke takwararta ta kasar Senegal a wasan farko da aka buga a kasar Qatar
Shaharraran mawakin Amurka Kenya West wanda ya canza sunansa zuwa Ye a hukumance, wanda ya tsaya takara a shekarar shugaban kasar Amurka a 2020 ya ce zai sake tsayawa takara ya kuma taka rawa a zaben 2024.
Zaben sabbin shugabannin uwar kungiyar Fulani makiyaya ta “MIYETTI ALLAH” ya bar baya da kura don daya daga ‘yan takara ya ce bai amince da sakamakon zaben ba.
Gwamnatin jihar Inugu tare da hadin gwiwar hukumar raya kasashe ta Faransa, AFD, zata kashe kimanin dala miliyan hamsin don samar da ruwan sha a fadin birnin Inugu, babban birnin jihar.
Wadansu ‘yan bindiga sun kai hari a wani sansanin sojoji da ke wani gari a arewa maso gabashin Najeriya inda suka kashe sojoji tara da ‘yan sanda biyu da fararen hula a ranar Lahadin da ta gabata a cewar majiyoyin tsaro da mazauna yankin, a wani sabon rikici da ya barke a yankin.
Sama da mutane 100 da suka hada da mata da yara ne aka yi garkuwa da su a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki wasu kauyuka hudu a jihar Zamfara da ke arewa maso gabashin Najeriya jiya Lahadi, kamar yadda kwamishinan yada labarai da mazauna yankin suka bayyana.
Hukumomin Jamhuriyar Nijer sun kama wasu fitattun mawakan Najeriya lokacin da su ke kokarin hada takardu don samun fasfon kasar ta Nijer da nufin zuwa kasashen turai.
Majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya ta dukufa ga binciken ayukkan Sojin kasar da manufar kara shiryawa wasu ayukkan a shekara mai zuwa.
Babban kwamandan rundunar tsaron sibil defence, Farfesa Ahmad Abubakar Audi, ya ce mata sun fi mayarda hankali a kan aiki idan aka basu dama shi yasa hukumar NSCDC ta kafa punduna ta musamman don taimakawa matan da su suka fi tagayyara idan aka fuskanci wani tashin hankali.
Tsarin narkewar abinci a ciki ya haɗa da sashin hanji ko gastrointestinal ko abunda ake kira GI, cikin mutum, ƙanana da manyan hanji, da gabobi kamar su hanta, dake taka muhimmiyar rawa wajen mai da abincin da muke ci ya zama mai amfani ga jiki.
‘Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin jam’iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu yayi alkawarin ci gaba da inganta harkokin noma da samarwa matasa ayyukan yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiwatar.
A yayin da majalissar dinkin duniya ta ware ranakun 13 zuwa 16 a matsayin makon fahimtar juna tsakanin mabanbanta addinai da kabilu, malaman addinin Kirista a jahar Kaduna sun karrama wani matashi da ya haddace al-qur'ani.
A yayin tashar talabijan Arise TV ta nemi afuwa game da yada labarin karya kan Tinubu, Shugaban hukumar NBC, Balarabe Ilellah, ya ce NBC ta dauki wannan matakin ne don ya zama jan kunne ga sauran kafafen yada labarai.
Domin Kari