Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilai Ta Soma Binciken Ayukkan Rundunar Sojin Najeriya


Rundunar sojin Najeirya
Rundunar sojin Najeirya

Majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya ta dukufa ga binciken ayukkan Sojin kasar da manufar kara shiryawa wasu ayukkan a shekara mai zuwa.

Hakan na faruwa ne lokacin da matsalolin rashin tsaro ke ci gaba da ta'azzara a wasu yankunan kasar inda jama'a ke ta kokawa.

Bisa ga yadda matsalar rashin tsaro ke ci gaba da wanzuwa a wasu yankunan Najeriya, fatar akasarin jama'a ta rataya ne kan jami'an tsaron kasar wajen kare rayuka da dukiyoyinsu.

Rundunar Sojin Najeriya ita ce ke sahun gaba wajen kare rayukan ‘yan kasa daga salwanta, kuma da yawa rundunar na cewa tana kokarin saukar da nauyin da ke kanta a wannan haujin.

Rundunar sojin Najeriya
Rundunar sojin Najeriya

Akan hakan ne ma majalisar wakilai ta Najeriya ta soma binciken ayyukan rundubar a ko'ina cikin fadin kasar da zummar sanin ayyukan da ta gudanar a wannan shekara domin duba yuwuwar amincewa da ayyukan da ta tsara gudanarwa a shekara mai zuwa ta 2023.

Wakili a kwamitin majalisar akan ayukkan soji Arch. Ibrahim Almustapha shi ne ya wakilci shugaban kwamitin Abdulrazak Namdas a ziyarar kwamitin a yankin rundunar soji ta takwas da ke Sakkwato.

Yace sun je ne su ganewa idanunsu abinda rundunar ta aiwatar da kudin da aka bata damar kashewa a wannan shekara kuma su saurari jami'an sojin in akwai wasu matsaloli da kwamitin zai iya taimakawa akai. Kuma gefen aikin da suke yi na fita daji a wannan yanki mai matsalar rashin tsaro sun lura ana samun sauki.

Yace cikin wannan shekara rundunar yanki na takwas da ya kunshi jihohin Sakkwato, kebbi , Zanfara da Katsina suna gudanar da ayyuka na aikatau kusan arba’in da shida kuma mafi yawancin su anyi kusa kammala su.

A bangare daya kuwa duk da ayyukan da rundunar Sojin ke gudanarwa matsalar rashin tsaro na ci gaba da yin barazana ga rayukan jama'a duk da nasarar da ake samu akan ‘yan ta'adda a wasu sassan kasar.

A yankin gabashn Sakkwato kananan hukumomin Isa, Sabon Birni da Illela kowace rana suna fuskantar hare hare daga ‘yan ta'adda.

Wakilin jama'ar Sabon Birnira majalisar dokokin kasar Aminu Almustapha Boza yace su har yanzu ba su ga kokarin da ake cewa ana yi ba na dakile ayukkan ‘yan ta'adda.

Yace a shekarun da Sojojji suka yi suna aiki a yankin Sabon Birni jama'a ba su ga dan ta'adda guda da sojojin suka kashe ba amma su an kashe su da yawa kuma yana da hujjar fadin haka.

Ya kara da cewa kamata ya yi a kara baiwa ‘yan sanda kudi da kayan aiki na zamani da kwarin guiwa ya tabbata zasu fi yin kokari wajen fada da ‘yan ta'adda.

Samun dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali babbar fata ce ta ‘yan Najeriya domin ta hakan ne kadai za a iya samun gudanar da lamurra cikin nasara da kawo ci gaban kasa.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG