Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZAMFARA: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutane Sama Da 100


Wasu masu garkuwa da mutane
Wasu masu garkuwa da mutane

Sama da mutane 100 da suka hada da mata da yara ne aka yi garkuwa da su a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki wasu kauyuka hudu a jihar Zamfara da ke arewa maso gabashin Najeriya jiya Lahadi, kamar yadda kwamishinan yada labarai da mazauna yankin suka bayyana.

Sace-sacen mutane dai ya zama ruwan dare a yankin arewa maso yammacin Najeriya yayin da wasu gungun ‘yan bindiga ke sace mutane daga kauyuka da manyan tituna da gonaki don neman kudin fansa daga ‘yan uwansu.

Sama da mutane 40 ne aka sace daga kauyen Kanwa da ke karamar hukumar Zurmi a Zamfara, kamar yadda kwamishinan yada labarai na Zamfara Ibrahim Dosara da wani mazaunin garin su ka bayyana.

An kuma yi garkuwa da wasu 37, galibi mata da kananan yara a unguwar Kwabre da ke karamar hukumar, kamar yadda mazaunin garin da ya ki bayyana sunansa saboda dalilan tsaro ya ce.

“A yanzu haka kauyen Kanwa babu kowa, ‘yan bindigar sun raba kansu gida biyu kafin suka far wa al’umman yankin, suka yi garkuwa da yara ‘yan shekara 14 zuwa 16 da mata.”

A yankin Yankaba da Gidan Goga na karamar hukumar Maradun, an yi garkuwa da akalla mutane 38 a lokacin da suke aikin gonakinsu, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.

Kwamishinan yada labarai Dosara ya zargi ‘yan bindigar da yin amfani da wadanda aka sacen a matsayin kariya daga sojojin sama da suka kai masu hari.

XS
SM
MD
LG