Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2023: Ban Ga Yadda Tinubu Zai Iya Lashe Zabe Ba - Babachir David Lawan


Babachir David Lawan
Babachir David Lawan

Madugun kamfen din samun tikitin dan takarar APC Bola Tinubu, Babachir David Lawan ya fito karara ya ce bai ga yadda Tinubu zai lashe zaben 2023 ba tun da bai dauki kirista mataimaki ba.

David Lawan wanda a yanzu ya ce shi da jama’ar sa na ganawa da sauran manyan ‘yan takara, ya nuna cewa, Tinubu ya yi biris da shawarar da su ka ba shi.

Babachir wanda tsohon sakataren gwamnatin Najeriya ne, ya fito da wasu kundaye da ya ce rahotonnin bayanai ne filla-filla na hanyar lashe zabe da ya gabatarwa Tinubu a London amma da Tinubu ya dawo sai ya ayyana Kashim Shettima a matsayin mataimakin takara.

A ra’ayin Lawan, inda Tinubu ya tuntubi kiristocin arewa da tayin wasu mukamai za su bi tafiyar amma yanzu lokaci ya kure.

Dangane da salon da Tinubu ya dauka kwanan nan inda ya gana da kungiyar mabiya addinin kirista CAN ya na mai cewa matar sa da ‘ya’yan sa kiristoci ne, Babachir ya ce hakan ba zai yi wani tasiri ba.

Kamfen din 2023 ya fara zafi inda masanin siyasa na jami’ar Abuja Dr.Sadik Abba ya zayyana jam’iyyar Leba ta babban dan takarar adawa Peter Obi da tamakar narkakkiyar jam’iyyar CPC ta shugaba Buhari ne da kan samu magoya baya daga bangare daya.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG