Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

QATAR 2022: Saudiyya Ta Yi Wa Argentina Bazata


Yan wasan kwallon Saudiyya a Qatar
Yan wasan kwallon Saudiyya a Qatar

Saudiyya ta samu gagarumar nasara yau Talata bayan da ta doke Argentina da ci 2-1 a wasansu na farko a gasar cin kofin duniya ta maza a Qatar.

Kasar Argentina ta shiga gasar ne a matsayi na uku a duniya, inda Saudiyya ke matsayi na 51.

Lionel Messi ne ya zura wa Argentina kwallo a minti na goma da bugun fenareti, kuma Argentina ce ke da iko a wasan duk da cewa an yi watsi da kwallaye da dama ta hanyar buga kwallo a wasan waje.

Lionel Messi
Lionel Messi

Sai dai Saudiyya ta yi saurin mamaye wasan a karo na biyu, yayin da a cikin mintuna 48, Saleh Alshehri ya zura kwallo.

Bayan mintuna biyar kuma Salem Aldawsari ya sake zurawa Saudiyya kwallo.

Salem Aldawsari
Salem Aldawsari

Mai tsaron ragar Saudiyya Mohammed Alowais ne ya taimaka wajen samun nasarar ta hanyar dakatar da wasu damammaki da dama a cikin mintunan karshe yayin da Argentina ta yi kokarin rama kwallon.

Argentina za ta yi kokarin dawowa ranar Asabar lokacin da za ta kara da Mexico a wani wasan rukunin C. Yayinda Saudiyya kuma za ta kara da Poland.

XS
SM
MD
LG