Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kaddamar da bude tagwwayen rijiyoyin albarkatun man fetur na Kolmani da suke jihohin Bauchi da Gombe.
Gudanar da aikin bude rijiyoyin man shi ne ya kawo tabbacin samun albarkatun man fetur da kuma iskar gas don kasuwanci.
A jawabinsa shugaba Buhari ya ce wannan muhimmiyar rana ce a tarihin kasar Najeriya ta fuskar tattalin arziki da zai kawo bunkasa tattalin arziki musamman samun albarkatun man fetur da ya ke kwance a kan hanyar kogin Benue musamman a jihohin Bauchi da kuma Gombe.
Shugaba Buhari ya kara da cewa, man fetur da iskar gas zasu kasance kan gaba a wajen aiwatar da kasafin kudin kasa da hakkan ya zamo wajibi na ganin an ci gaba da fadada wannan sashe na tattalin arziki. Buhari ya kuma yaba da kokarin kamfanin NNPC sabili da nasarar da aka cimma na tono man fetur din.
Wannan ne karon farko da ake haƙo man fetur a Arewacin Najeriya.
Gabanin gano arzikin man fetir a Arewacin kasar, yankin Neja Delta kadai ke da arzikin man fetur a Najeriya.
Saurari rahoton cikin sauti: