Kungiyoyin da ke dauke da makamai sun yi kaca-kaca da yankin arewa maso yammacin kasar inda suke yin fashi ko kuma yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, kuma tashe-tashen hankula na karuwa ganin yadda jami'an tsaro masu karamin karfi suka kasa dakile hare-haren da ake kaiwa.
Hakan dai ya haifar da fargabar ko mazauna yankin za su iya kada kuri’a a zaben shugaban kasa da za a gudanar a watan Fabrairu domin zaben wanda zai gaji shugaba Muhammadu Buhari, wanda tsarin mulkin kasar ya haramtawa sake tsayawa takara.
Wasu mazauna garin biyu sun ce wasu ‘yan bindiga a kan babura ne suka isa unguwar Magami Tandu da ke karamar hukumar Kaura Namoda a yammacin Laraba inda suka yi ta harbe-harbe.
Sun dauki galibin mata ne da suke gudanar da bukin Maulidin Manzon Allah SAW wanda ake gudanarwa tsakanin karshen watan Satumba zuwa karshen watan Nuwamba a jihohin Musulmin Arewacin Najeriya, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.
“A kullum ana kashe-kashe ko sace-sacen mutane, wanda hakan ke sa mu mu rasa mazaunin mu. Don Allah ku gaya wa gwamnati ta yi mana adalci.” Inji Abdulkarim Haruna, wanda shi ma aka yi garkuwa da matarsa.
Mazauna garin sun ce an kashe mutane 19 a ranar Talata a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a kauyen Ryuji da ke karamar hukumar Zurmi ta Zamfara, da ke makwabtaka da Kaura Namoda.
Ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu ba, domin jin ta bakinsa.
~ REUTERS