Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Ziyarci Jihar Filato Don Yakin Neman Zabe


APC a Filato.
APC a Filato.

‘Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin jam’iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu yayi alkawarin ci gaba da inganta harkokin noma da samarwa matasa ayyukan yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiwatar.

Bola Ahmed Tinubu da dubban magoya bayan jami’iyyar APC sun hallara ne a Jos, fadar Jahar Filato don kaddamar da fara yakin neman zabe na shakara ta dubu biyu da ishirin da uku.

Tinubu wanda ya dauki tsawon lokaci yana yabawa da ayyukan da shugaban kasa Muhammdu Buhari yay,i ya kuma ce gwamnatinsa zata samadda cibiyoyin habaka harkokin noma don samarwa kasa abinci.

APC a Filato
APC a Filato

Shima mataimakin ‘dan takarar shugaban kasa na APC, Sanata Kashim Shettima ya yaba ne da tsaro da suka samu a yankinsa na Borno, Adamawa da Taraba.

Waasu da suka halarci gangamin sun bukaci shugabannin su cika alkawuran da suke yi wa talakawa.

APC a Filato
APC a Filato

Alhaji Jamilu Baba, wani kusa a jami’iyyar APC a Jahar Filato ya bayyana cewa mafi yawan wadanda suka halarci gangamin baki ne, amma su ‘yan gida sun kaurace wa taron saboda mastala dake tsakanin magoya bayan jami’iyyar

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:18 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG