Yanzu dai tawagar kwallon kafar ‘Black Stars’ ta Ghana ta fice daga gasar cin kofin duniya ta 2022 da ake gudanarwa a Qatar, bayan da kasar Uruguay ta yi nasara a kanta da ci 2-0 a ranar Juma’a.
Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da Musulmai 19 masu ibada bayan sun kai hari a wani masallaci a yankin arewa maso yammacin Najeriya mai fama da tashin hankali, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana a jiya Lahadi.
Jakadan Najeriya a kasar Rasha, Farfesa Abdullahi Yibaikwal Shehu, ya ja hankalin sabbin daliban Najeriya da suka iso kasar Rasha a bisa tsarin tallafin karatu tsakanin Najeriya da kasar Rasha na shekarar 2022 zuwa 2023.
A wannan makon, shirin Lafiyarmu zai maida hankali ne a kan ranar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki wato AIDS wacce aka ware 1 ga watan Disamba don wayar da kan al’umma a kan cutar Musamman yadda kwararru suka ce ana ci gaba da samun rashin daidaito a yaki da cutar.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta bayyana ranar Litinin 12 ga watan Disemba a matsayin ranar da za’a fara karbar katin zabe.
A daidai lokacin da ake ganin kamata ya yi Najeriya ta kara himma wajen aikin cimma kudurorin nan 17 na raya kasashe wato SDGs na MDD don kawo karshen talauci baya ga tabbatar da wadata ga kowa da kowa, Najeriyar da ma MDD sun rattaba hannu a kan tsarin hadin gwiwa na shekarar 2023 zuwa 2027.
Ganin yadda aka fara samun matsaloli a wasu wuraren yakin neman zaben jam'iyyu ya sanya hukumar wanzar da zaman lafiya ta jahar Kaduna da hadin gwiwar wasu kungiyoyi, kiran taron masu ruwa da tsaki don gudanar da yakin neman zabe, da kuma zabubbuka lafiya a fadin jahar.
Hukumar yaki da cutar kanjamau ta Majalisar Dinkin Duniya (UNAIDS), ta ce mutane dubu 3,157 ne suka kamu da cutar kanjamau a kasar Kamaru a shekarar da ta gabata. Wannan ya nuna cewa an samu ci gaba wajen yaki da wannan cutar.
Hukumar kwastam ta ce a fili ta ke gudanar da gwanjan kaya kuma kowa zai iya shiga yanar gizo ya ga yanda a ke gudanar da cinikin.
Yarima William na masarautar Burtaniyya da matarsa Kate sun tashi zuwa Amurka a ranar Laraba don kai ziyara a karon farko cikin shekaru takwas.
Kamaru da Serbia sun tashi da kunnen doki 3-3 ranar Litinin a gasar cin kofin duniya ta maza a Qatar, yayin da suke kokarin ci gaba da fatan tsallakewa zuwa matakin rukuni.
Babban jigon darikar Katolika Cardinal Richard Kuuia Baawobr kuma shugaban majalisan limaman darikar katolika a nahiyar Afrika, ya rasu a jiya a birnin Roma na kasar Italiya.
Ana zargin 'yan banga sun kashe mutane sama da goma sha biyu a yankin Kukana zuwa Jatau da ke karamar hukumar Bali, sun kuma kona gidajen sullubawa dake zama a rugar da kuma kore musu garken shanu sama da goma a rugar.
Kungiyoyin rajin shugabanci na gari a jihar Kano sun yi Allah wadai da kalaman tunzura Jama’a na baya-bayan nan da suka fito daga bakunan shugabannin Jam’iyyun APC da NNPP na jihar ta Kano.
A ranar Lahadin da ta gabata ne wani jami'in gwamnatin jihar Legas ya fitar da jerin sunayen da aka tantance na wasu kamfanoni da ke karkashin jagorancin kasar Portugal Mota-Engil da wasu kamfanoni biyu na kasar China don gina gadar da za ta ci dalar Amurka biliyan 2.5.
Wata zaftarewar kasa da ta auku a Yaounde babban birnin kasar Kamaru a ranar Lahadin da ta gabata, ta kashe akalla mutane 14 da ke halartar wata jana'iza, in ji gwamnan yankin.
Gwamnatin kasar Ghana ta kudiri aniyar kashe jimillar kudin Ghana Cedi miliyan dari biyu da biyar da digo hudu (GH¢205.4) a shekarar 2023, duk da bashin da ake bin ta.
Domin Kari