Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

QATAR 2022: Rashin Gogewa Ne Dalilin Ficewar Tawagar ‘Black Stars’ Ta Ghana Da Wuri – Manazarta


Black stars
Black stars

Yanzu dai tawagar kwallon kafar ‘Black Stars’ ta Ghana ta fice daga gasar cin kofin duniya ta 2022 da ake gudanarwa a Qatar, bayan da kasar Uruguay ta yi nasara a kanta da ci 2-0 a ranar Juma’a.

Dan wasan Ghana, Andre Ayew ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron gida, daga baya ‘yan wasan Uruguay suka zura kwallaye biyu a ragar Ghana.

Sai dai har wa yau, manazarta na tofa albarkacin bakinsu kan ficewar kasar da wuri, inda wasu suka ba da dalilin cewa rashin gogewa daga bangaren ‘yan wasa da kocinsu, Otto Addo ne ya janyo hakan.

Coach Otto Addo
Coach Otto Addo

A taron manema labarai da aka gudanar gabanin wasan Ghana da Uruguay, mai horas da ‘yan wasan Ghanan, Otto Addo da kansa ya tabbatar da cewa ‘yan wasansa ba su da gogewa a gasar cin kofin duniya domin mafi yawancinsu wannan ne gasarsu ta farko.

Bayan Ghana ta doke Koriya ta Kudu a wasa ta biyu da ci 3-2, sai al’ummar Ghana suka samu kwarin gwiwar samun nasara a kan Uruguay a wasa na gaba, amma sai ya kasance akasin haka ne ya faru, sabili da rashin gogewa da jajircewa, kamar yadda shugaban sashen wasanni na Gaskia TV, AbdulWahab Jawando ya nuna cewa, da ‘yan wasan da kocin sun yi la’akari da kuskuren da suka yi a baya, suka gyara a wasa na gaba da ficewarsu bai faru ba. Yace, har yanzu gogewar mai horas da ‘yan wasan da saura.

Yan wasan kwallon Ghana
Yan wasan kwallon Ghana

Mai sharhi a kan harkar kwallon kafa, Yusuf Alhassan Uthman, ya amince da cewa rashin gogewar kocin Ghana ta taimaka wajen ficewar kasar daga gasar. Yace, wasu canjin ‘yan wasa da ya yi basu dace ba, haka kuma kocin ba shi da takamaiman dabara ko tsarin wasa daya da ya amince da shi, wanda yake sai lallai yanayin wasa ya canja sannan shi ma ya canja wani tsarin amma, yana sa ran zai kara gogewa a nan gaba.

Abdulhanan Adam dan jarida ne kuma mai sharhi ne na wasanni. Ya ce canje-canjen ‘yan wasa da koci Otto Addo ya yi a wasannin da Ghana ta buga ba su dace ba.

A wani labari mai alaka da wannan, rahotanni na cewa dan wasan Ghana, Andre Dede Ayew, ya garzaya zuwa asibiti bayan da Ghana ta buga da Uruguay, domin duba ‘yarsa da ta fadi a lokacin wasan.

Yarinyar, ‘yar shekaru 7 ta fadi ne, sakamakon rashin cin fanareti da mahaifinta ya yi, a wasan da kasar Uruguay ta doke Ghana da ci 2-0.

A halin yanzu yarinyar ta samu sauki kuma an dawo da ita gida daga asibiti.

Saurari rahoton Idris Abdullah Bako :

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

XS
SM
MD
LG