Maharan sun far wa masallacin ne da ke kauyen Maigamji da ke jihar Katsina a lokacin sallar magariba a ranar Asabar din da ta gabata, inda suka yi garkuwa da su bayan sun harbe da kuma raunata limamin da wani mai ibada, in ji kakakin ‘yan sandan yankin Gambo Isah.
“Tuni mutanenmu suka hada kai suka bi ‘yan bindigar inda suka yi nasarar ceto shida daga cikin masu ibada daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su, yayin da ake kokarin kubutar da sauran 13 da suka rage.”
Ya kara da cewa mutanen biyu da suka jikkata suna jinya a asibiti.
Yankin Arewa maso Yamma da tsakiyar Najeriya na fuskantar ta’addanci daga wasu gungun ‘yan bindiga wadanda ke kai farmaki kauyukan suna satar shanu da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa tare da kona gidaje bayan kwashe kayayyaki.
Yawanci akan saki wadanda aka yi garkuwa da su ne bayan an biya kudin fansa ga kungiyoyin da ke fakewa a dajin Rugu mai fadin gaske. Ya ratsa jihohi hudu a arewa maso yammacin Najeriya ciki har da Katsina.
A watan da ya gabata, an kashe mutane 15 tare da jikkata wasu da dama a wasu hare-haren ‘yan bindiga da suka kai a kauyukan jihar Kaduna mai makwabtaka da jihar, kamar yadda hukumomi suka ce.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dai na fuskantar matsin lamba kan ya kawo karshen tashe tashen hankula kafin ya bar mulki a shekara mai zuwa a karshen wa'adinsa na shekaru takwas.
Ana kara nuna damuwa game da kawance a yankin arewa maso gabas tsakanin 'yan fashi da masu jihadi da suka shafe shekaru 12 suna tada kayar don kafa tsarin Halifanci.