A wata sanarwa da ke da sa hannun sakatare janar darikar katolika a reshen nahiyar Afrika, Andre Leon Simonart, ta ce jigon a darikar katolika ya rasu ne bayan tiyata a zuciya da aka yi masa a wani asibiti mai suna Agostino Gemelli University Hospital da ke Roma a kasar Italiya.
Kafin a sanar da rasuwarsa sai da shugaban darikar Katolika a duniya Pope Francis ya bukaci da ayi masa addua.
Sakatarin ya jajantawa mabiya darikar Katolika a sassan duniya da abokan arziki bisa wannan babban rashi.
A watan Yulin bana ne aka zabi Cardinal Richard a matsayin shugaban SECAM wato majalisan limaman darikar katholika a nahiyar Afrika.
Shugaban ya yi fice wajen kare hakkokin bil Adama musamman masu fama da matsalar tabin hankali. Shekaru shidda da suka gabata Cadinal Richard ya kaddamar da wani shiri na musamman na kula da kiwon lafiyan masu fama da laluran tabin hankali da iyalansu suka yi watsi da su.
An haifi Cardinal Richard Kuuia Baawobr a ranar 21 ga watan Yunin shekarar dubu da dari tara da hamsin da tara a gundumar Nandon da ke jihar arewa maso yammacin kasar Ghana.
Kasancewa Ghana kasa ce da akwai karfin halaka da fahimtar juna tsakanin addinai musamman musulmai da krista ya sa Muryar Amurka ta tuntubi daya daga shugabannin addini Islama kuma mamba a majalisan wanzar da zaman lafiya a kasar Sheikh Salman Alhassan, wanda yace ko shakka babu Ghana da ma nahiyar Afrika sun yi rashi babba saboda Cardinal Richard mutum ne mai fafutukan kare hakkin bil'adama musaman masu fama da tabin hankali kuma ya na daga cikin masu neman zaman lafiya a nahiyar.
Shugaban darikar Cardinal Richard ya rasu ya na da shekarau 63 da haihuwa a duniya.
Saurari rahoton Hamza Adam cikin sauti.