Wannan ne karon farko da William da Kate zasu kai ziyara ketare tun bayan rasuwar Sarauniya Elizabeth ta biyu.
Ziyarar na zuwa ne 'yan kwanaki gabanin wani babban bikin bayar da lambar yabo da za a yi, inda kanin William da ke birnin Los Angeles, Yarima Harry da matarsa ba-Amurkiya Meghan zasu ja hankalin jama’a, kuma kafin a saki wani zangon shirin talabijin na Netflix.
"Iyalin sarauta, Iyalai ne masu cike da gasa a tsakaninsu, abinda marubucin tarihin rayuwar sarki Andrew Morton ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters kenan.
Da farko dai William da Kate za su ziyarci Boston don halartar bikin bayar da lambar yabo ta muhalli ta Earthshot da yariman ya kafa.
A shekarun baya, da suka kai ziyara Amurka a watan Nuwamban 2014, William da matarsa sun kasance bakin shugaban kasa Barack Obama a lokacin da yake fadar White House.
A ziyararsu ta kwanaki uku, William mai shekaru 40, da Kate ita ma mai shekaru 40, za su ziyarci dakin karatu da kayan tarihi na John F. Kennedy, inda za su gana da Caroline Kennedy diyar tsohon shugaban Amurka wadda a yanzu ita ce jakadiyar Amurka a Australia.