Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KAMARU: Zaftarewar Kasa Ta Kashe Akalla Mutane 14 Da Suka Halarci Wata Jana'iza A Yaounde


Zaftarewar kasa.
Zaftarewar kasa.

Wata zaftarewar kasa da ta auku a Yaounde babban birnin kasar Kamaru a ranar Lahadin da ta gabata, ta kashe akalla mutane 14 da ke halartar wata jana'iza, in ji gwamnan yankin.

Mutane da dama ne su ka halarci jana'izar a filin wasan kwallon kafa a gindin wani shingen kasa mai tsayin mita 20, wanda ya rufta a saman su, kamar yadda shaidu suka shaida wa Kamfanin dillancin labaran Reuters.

"Mun yi ta daukan gawarwaki zuwa dakin ajiyar gawa na babban asibitin tsakiya, yayin da ake ci gaba da cigiyar neman wasu mutane, ko gawarwakinsu," in ji Naseri Paul Bea, gwamnan yankin tsakiyar Kamaru.

Yaounde na daya daga cikin birane da ake yawan fuskantar ruwan sama mai yawa a Afirka kuma mai dimbin tuddai masu tudun gaske.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya janyo ambaliyar ruwa da dama a fadin kasar a bana, lamarin da ya raunana ababen more rayuwa tare da raba dubbai da muhalansu.

A watan da ya gabata Najeriya makwabciyar Kamaru, ta fuskanci ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekaru goma, inda daruruwan mutane suka mutu sannan akalla gidaje 200,000 suka lalace.

~ Reuters

XS
SM
MD
LG