Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GHANA: Gwamnati Ta Gabatar da Kasafin Kudin 2023 Ga Majalisar Dokoki


Majalisar Dokokin Ghana
Majalisar Dokokin Ghana

Gwamnatin kasar Ghana ta kudiri aniyar kashe jimillar kudin Ghana Cedi miliyan dari biyu da biyar da digo hudu (GH¢205.4) a shekarar 2023, duk da bashin da ake bin ta.

Ministan Kudi Ken Ofori-Atta ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da bayanin kasafin kudin 2023 ga majalisar dokokin kasa.

Ministan harkokin kudin Ghana, Ken Ofori-Attah, yayin da yake bayanin kasafin kudin shekarar 2023 ga Majalisar dokoki ta kasa yace, “Jimlar kudaden shiga da tallafi da aka yi hasashe, za su kai miliyan GH¢143,956, kuma ta hanyar matakan samun kuɗin shiga na dindindin ne - galibi matakan haraji. Jimlar kudaden da za mu kashe, ciki har da biyan bashi, ana hasashen zai kai miliyan GH¢205,431”.

Ken-Ofori Attah
Ken-Ofori Attah

Abin da hakan ke nufi shi ne, hasashen samun kudaden shiga da kuma kudaden da za a kashe, za a samu gibin miliyan GH¢ 61.9.

Ministan ya kawo matakai 13 na rage kashe kudaden gwamnati. Daga ciki akwai; rage kashi 50% na kudaden da hukumomin gundumoni da birane suke kashewa a man fetur da sauran harkokinsu; rage sayen motocin gwamnati; rage tafiye-tafiyen jami’un gwamnati; za a dawo da harajin da aka daukewa wasu kamfanunnukan kasashen waje sanna kuma babu daukan sabbin ma’aikata a shekarar 2023.

Domin tara kudaden shiga na cikin gida, Ministan Kudi, Ofor-Attah ya ce, "za a dora hakan ne kan ajanda bakwai da nufin daidaita fannin tattalin arziki da kuma hanzarta kawo sauyi ga tattalin arzikin. Daga cikinsu akwai, kara harajin VAT da kashi 2.5%; gwamnati za ta rage yawan harajin e-levy daga kashi 1.5%; gwamnati za ta inganta fitar da kayayyaki zuwa ketare da kuma karfafa amfani da na cikin gida."

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Ayawaso ta Arewa na jami’iyar adawa ta NDC, Hon. Yussuf Jajah, ya gayawa muryar Amurka cewa, wannan kasafin kudin na sanarwa al’ummar Ghana, cewa wahalar da aka sha a shekarar 2023 zata fi wadda aka sha a shekarar 2022.

Al’ummar Ghana har wa yau suna ji a jika yadda kasafin kudin 2022 ya jawo tsanani ga rayuwarsu. Wasu al’ummar kasa sun bayyana ra’ayinsu game da hakan, suka ce ya kawo musu kunci a rayuwarsu ne. Sai dai suna fatan wannan kasafin kudin ya kawo sauki.

Mataimakiyar darektan sadarwar jam’iyar NPP mai ci, Hajiya Rabi Salifu a na ta bangaren, tace wahalhalun da ake fama da su ba Ghana kadai bane, duniya gaba daya ne.

Hon Jajah, ya yi bayanin dalilin da ya sa suka halarci bayanin kasafin kudin, sabanin ikirarin da suka yi cewa ba za su halarta ba idan, lallai Mista Ken Ofori-Atta ne zai gabatar. Yace, sun samu labarin cewa ministan yace zai yi murabus bayan ya yi bayanin kasafin kudin, amma, su suna jira idan bai yi ba, za su jefa kuri’ar tsige shi.

Saurari rahoton Idris Abdullah Bako cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG