Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Mota-Engil Na China Na Cikin Jerin Kamfanonin Da Aka Tantance Don Gina Gadar Legas


Wata gada a Legas
Wata gada a Legas

A ranar Lahadin da ta gabata ne wani jami'in gwamnatin jihar Legas ya fitar da jerin sunayen da aka tantance na wasu kamfanoni da ke karkashin jagorancin kasar Portugal Mota-Engil da wasu kamfanoni biyu na kasar China don gina gadar da za ta ci dalar Amurka biliyan 2.5.

Mota-Engil ya hada gwiwa ne da Kamfanin Sadarwa da Gine-gine na kasar China da kuma Kamfanin Titi da Gada na kasar China a neman kwalgilar.

Kamfanin China Gezhouba Group, da China Geo-Engineering Corporation, tare da hadin gwiwar kamfanin gine-gine na China Civil Engineering Construction Corporation su ne sauran kamfanonin biyu da aka tantance.

Za a gina gadar wadda za ta kasance ta hudu da aka gina, don rage cunkoso a gadar da ake da ita ta Third Mainland Bridge kuma aikin zai ci kusan dala biliyan 2.5.

Sauran kananan gadoji da suka hada tsibirin Legas da babban yankin jihar Legas sun hada da gadar Eko mai tsawon kilomita 1.35 da Julius Berger Nigeria Plc ta gina da gadar Carter da aka gina a 1901.

Idan aka kammala aikin gada ta 4, za ta kasance wani bangare na manyan tsare-tsare na sufuri da Najeriya ke sa ran bunkasa gudummawar kayayyakin more rayuwa a kasar zuwa akalla kashi 70% na ci gaban tattalin arzikin kasa daga kashi 25 na yanzu.

Jubril Gawat, babban mai magana da yawun gwamnan jihar Legas ya ce za a sanar da wanda ya yi nasara kafin karshen shekara.

~ REUTERS

XS
SM
MD
LG